✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shayi

Wani mutum ne ya je shan shayi sai ya ce kar a ba shi mai zafi, a daga, domin bakinsa da kuraje. Sai mai shayi…

Wani mutum ne ya je shan shayi sai ya ce kar a ba shi mai zafi, a daga, domin bakinsa da kuraje. Sai mai shayi ya ji kamar ya ce kar a daga. Yana debowa sai ya mika masa haka nan. Mutumin yana kurba sai ya furzar don zafi. Dama mai shayin yana sanye da takalman roba sau-ciki, kawai sai ya juye masa shayin cikin takalmi. Mai shayi ya fice a guje yana cewa: “A taimaka!”
Daga Salisu A.