✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ba ta da hurumin binciken bidiyon zargin Ganduje – Barista Dalhatu

Wani lauya mai rajin kare hakkin dan Adam a Jihar Kano, Barista Usman Dalhatu ya soki Majalisar Dokokin Jihar Kano bisa tsoma baki kan  binciken…

Wani lauya mai rajin kare hakkin dan Adam a Jihar Kano, Barista Usman Dalhatu ya soki Majalisar Dokokin Jihar Kano bisa tsoma baki kan  binciken gaskiyar lamari game da hoton bidiyon da ake zargin Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da karbar rashawa.

Barista Dalhatu ya shaida wa Aminiya cewa kasancewar wannan lamari ya shafi aikata wani laifi, hakki ne na kotu ta gano gaskiya tare da yanke hukunci a kai. “Idan an samu cewa an aikata wani laifi to hurumi ne na kotu ta binciko gaskiyar lamari tare da yanke hukunci,” inji shi.

Duk wani abu da ya shafi hukunci “Gwamna ya riga ya kai maganar kotu, amma majalisa ta dakatar da duk wani abu da ya shafi hukunci ko abin da ya shafi shaida a zo a ji wane ya aikata laifi ko bai aikata ba abu ne da ya shafi kotu kai-tsaye,” inji shi.

Barista Dalhatu ya yi karin haske da cewa “Hurumin da majalisa take da shi shi ne bayan kotu ta yanke hukunci misali ta samu Gwamna da laifi, to hurumin majalisa ne ta kafa kwamitin tsige Gwamna amma ba a yanzu da ake binciken gaskiyar lamari ba.”

Lauyan ya yi kira ga majalisar ta janye hannunta a cikin wannan magana ta bar wa kotu aikinta  “Ina fata majalisa za ta janye hannunta ta bar kotu ta gudanar da aikinta. Idan kin duba tun farko Gwamnan ya riga ya kai kotu cewa an bata masa suna, amma majalisar ta dakatar da shi ta ce ita ce za ta yi wannan aiki, ba daidai ba ne. Ina fata majalisar za ta bar Gwamnan ya ci gaba da abin da ya fara na kai kara gaban kotu, kuma ina neman majalisa ta manta da gayyato mutane don jin shaida, a bar wa kotu ta yi aikinta,” inji shi..

Majalisar Dokokin Jihar Kano dai ta kafa kwamiti mai wakilai bakwai don ya binciki gaskiyar hoton bidiyon da ake zargin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karbar rashawar kudin kasashen waje daga hannun wadansu ’yan kwangila.

Kafa kwamitin da majalisar ta yi ya biyo bayan gabatar da kudirin gaggawa da Mai tsawatarwa a Majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari wakilin Karamar Hukumar Warawa ya yi.

A lokacin da yake kafa kwamitin, Shugaban Majlaisar Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya ba kwamitin wa’adin wata guda ya gabatar da rahotonsa gaban majalisar. ’Yan kwamitin sun hada da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Baffa Babba Dan Agundi a matsayin Shugaban Kwamitin.