✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Koli ta Shari’a ta soki alakanta dakatar da Onnoghen da addini

Ashekaranjiya Laraba ce Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci reshen Jihar Kaduna ta mayar da martani ga masu sukar matakin dakatarwa da aka dauka a kan…

Ashekaranjiya Laraba ce Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci reshen Jihar Kaduna ta mayar da martani ga masu sukar matakin dakatarwa da aka dauka a kan Babban Jojin Najeriya, Walter Onnoghen.

A cewar majalisar, bai kamata lauyoyi su rika danganta addini ko kabilanci a kan batun dakatar da Mai shari’a Walter Onnoghen ba.

Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci reshen Jihar Kaduna da Sakatarensa Injiniya Abdurrahman Hassan ya wakilta a wajen ganawa da manema labaran bayan wani taro da mambobin majalisar suka yi a jihar, ya ce abin damuwa ne yadda wadansu lauyoyi ke danganta dakatar da Mai shari’a Onnoghen da addini domin yin hakan bai dace ba.

Don haka sai majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tabbatar adalci ya tabbata a kan duk wanda ya aikata laifi.

Ya ce “Mu abin da muke cewa shi ne, a yi adalci a kan batun domin ai wannan ba shi ne karon farko da ake sauke Babban Jojin Kasa ba. Baya ga haka muna cewa a bar doka ta yi aikinta.  Bai kamata Kotun Koli ta bar masu laifi suna aikata laifuffuka ba da sunan masu shari’a. Saboda haka muna bai wa masu danganta batun da kabilanci da addini shawarar cewa su daina, domin yin hakan, domin ba zai haifa wa kasar nan da mai ido ba.”

“Mu kwantar da hankalinmu tare da guje wa duk wani abu da ka iya raba kawunan al’ummar kasar nan. Muna yin kira ga al’ummar Musulmi su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda,” inji shi.

Majalisar ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi duk mai yiwuwa a bisa tsarin dokar kasar nan, domin  kawo karshen dambarwar.