✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makiyayi mai shekara 15 ya guntule hannun manomi a Bauchi

Makiyayin ya guntule hannun manomin ne bayan ya yi masa ta'adi a gona

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wani maakiyayi bisa zarginsa da yanke hannun wani manomi bayan ya shigar masa gonaki da dabbobinsa.

’Yan sandan sun ce sun kama matashin makiyayin ne mai shekara 15 mai suna Adamu Ibrahim, mazaunin kauyen Jital da ke kan hanyar Gombe a Jihar Bauchi.

Kakakin rundunar a Jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Bauchi.

Ya ce, “Jami’an ’yan sandan yankin sun kama Adamu Ibrahim dan kauyen Jital da ke kan hanyar Gombe a Jihar Bauchi bisa laifin shiga gona ba bisa ka’ida ba, ga yin barna da haddasa jin ciwo ta hanyar guntule hannun manomin.

“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya sha shiga gonakin mamacin da shanunsa a lokuta da dama yayin da yake kiwo. Kuma shi mai gonar ya yi ta kai qorafi wa mahaifin wanda ake zargin saboda kutsawa cikin gonakinsa na shinkafa da wanda ake zargin yake yi.

“Hakazalika, bincike ya nuna cewa a ranar 24 ga watan Agusta, 2023, wanda ake zargin yana dauke da sanda da kuma adda, ya kai shanunsa gonar wanda ya yanke wa hannu suka ci shinkafa, kuma suka lalata amfanin gonakin da har yanzu ba a tantance kiyasin kudinsu ba.

“Sakamakon haka aka samu rashin jituwa, inda wanda ake zargin ya daba wa wanda aka yanke wa hannun adda ya sareshi, a lokacin da ya nemi ya bar gonarsa. Ya sare hannun hagun mai gonar.

“Da samun wannan rahoton sai yan sanda suka bazama suka kuma dauki matakan kariya domin dakile duk wani abu da ka iya haifar da rikicin makiyaya da manoma a jihar, kuma suka kama wanda ake zargin.

“An garzaya da wanda aka jiwa rauni zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin kula da lafiyarsa, kuma yana karbar magani.”

Wakil ya ce Kwamishinan ’yan sandan Jihar CP Auwal Musa Mohammed,  ya gargadi makiyaya da su kauce wa kutsawa cikin gonakin mutane a jihar, sannan ya bayar da umarnin gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.