✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makwabci ya sace dan makwabci don neman kudin fansa

Ana zargin wani makwabci mai suna Nuhu Abubakar wanda aka fi sani da Yellow da ke gyaran wayar hannu a Kasuwar Waya da ke PZ…

Ana zargin wani makwabci mai suna Nuhu Abubakar wanda aka fi sani da Yellow da ke gyaran wayar hannu a Kasuwar Waya da ke PZ a Sabon Gari, Zariya da sace dan makwabcinsa domin neman kudin fansa.

Aminiya ta ziyarci unguwar da lamarin ya faru a inda mutane ke ta tururuwa don taya iyayen  yaron murna bayan Allah Ya bayyana shi.

Mahaifin yaron Malam Suleiman Haruna ya bayyana wa Aminiya cewa: “A ranar Lahadi 9 ga Yunin nan wato kimanin kwana 10 da suka wuce aka zo har gida aka dauke mini dana Muhammad dan shekara biyar da haihuwa, kuma har ga Allah ban zargi kowa ba. To bayan mun yi nema Allah bai sa mun gan shi ba, sai  muka dukufa ga rokon Allah. Muna cikin haka sai aka kira ni a waya cewa su ne suka dauke min yaro don haka in kawo  Naira miliyan hudu don a sako shi. Sai na ce ba ni da Naira miliyan hudu, sai suka ce duk da yawan shagunan da nake da su? Sai na ce ai kudin ba nawa ba ne, na banki ne kuma yanzu haka banki sun sa ni a gaba don in biya su kudinsu don haka ba ni da kudi. Sai suka ce to ia ga gidana na kusa da ni, in sayar mana. To tun daga nan na fara zargin wadanda ke da hannu a dauke mini yaro na kusa da ni ne, kuma sun san ni. Kuma duk inda na sa kafa sai su gaya min cewa ina wuri kaza, amma duk abin nan bai razana ni ba, abin da na sa a gaba shi ne rokon Allah.”

Ya kara da cewa: “Haka muka yi ta yi da su, da suka ga alama babu sauki ta wurina sai suka koma tuntubar mahaifiyar yaron inda suka ce ta biya Naira miliyan 2 maimakon Naira miliyan hudu da suka nema a wajena. Ita ma cikin ikon Allah sai ta jajirce ta nuna ba ta da kudi. Daga nan ne suka daina kira, muka ci gaba da rokon Allah.  Muna zaune kwatsam, sai Sarkin Unguwar Nagoyi ya kira ni in je ga sako an aiko wani direba daga Karamar Hukumar Toro ta Jihar Bauci. Ina zuwa sai Sarki ya shaida mini an tsinci wani yaro ne a can Bauchi kuma ga lambar waya da za a kira don a samu karin bayani. Bayan mun kira ne suka shaida mana wani yaro ne aka tsinta inda ya ce sunansa Muhammadu kuma a Unguwar Nagoyi yake a Zariya.

Nan take na sanar da ’yan sanda inda aka hada ni da dan sanda daya muka tafi Bauchi. Da isarmu dana na ganina ya taso a guje ya rungume ni hakan ya tabbatar wa jama’ar wurin lallai dana ne.”

Suleiman Haruna ya ce wata mata ce a Bauchi ta ce wani ne ya kai mata yaron gidanta ya ajiye lokacin da ba ta gida. Da ta koma ne ta samu yaron cikin wani yanayi. Bayan ta yi masa tambayoyi ne sai ta fahimci sato shi aka yi. Allah Ya sa yana da wayo inda ya shaida mata sunansa da unguwar da yake a Zariya.

Bayan ’yan sanda sun tsananta bincike ne aka gano makwabcin Suleiman Haruna a kasuwa mai suna Nuhu Abubakar Dan Bida da aka fi sani da Yellow yana da hannu a ciki.

DPO din ofishin ’yan sanda da ke Kofar Fada a Zariya Kasim Abdul ya tabbatar da faruwar lamarin.  Ya ce sun kama Abubakar Yellow, amma suna zargin wani abokin Yellow ne ya sace yaron kuma watakila da hadin bakinsa.