✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maniyyata 4,151 ne za su sauke farali bana daga Jihar Kebbi

Hukumar Jin Dadin Alhazzai ta Jihar Kebbi ta ce kimanin maniyyata 4,151 ne za su gudanar da aikin Hajjin bana daga jihar, kuma ta yi…

Hukumar Jin Dadin Alhazzai ta Jihar Kebbi ta ce kimanin maniyyata 4,151 ne za su gudanar da aikin Hajjin bana daga jihar, kuma ta yi masu kyakkyawar shiri don ganin sun gudanar da aikin Hajji cikin jin dadi tun daga nan Najeriya zuwa kasa Mai tsarki.
Bayanin haka ya fito ne daga Shugaban Hukumar Alhaji Abdullahi Imam Shema lokacin da yake zantawa da Aminiya a Birnin Kebbi.
Alhaji Imam Shema, ya ce aikin Hajjin bana daga a jihar zai zama abin alfahari don haka ya bukaci maniyyatan jihar baki daya su ba da goyon baya da hadin kai domin tabbatar da cewa an gudanar da aikin cikin nasara.
Ya yi kira ga mahajjatan su bi doka da oda kada su zubar da mutuncin jihar da kasarsu, su zama masu da’a a kowane lokaci har Allah Ya sa su gama aikin aikin Hajji lafiya. Sai ya bukaci su yi wa kasar nan addu’o’in Allah Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma Ya tona asirin masu aikata ta’asa a duk inda suke a duniya.