✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman doya kan nemi izinin ’yan ta’adda kafin shiga gonakinsu

Hatta wadanda ba su samu damar yin noma a bara ba, sun fara noma a bana.

A yayin da harkokin noma suke kankama, wadansu manoman da aka tarwatsa su a garuruwansu a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, sun yanke shawarar tattaunawa da ’yan bindiga don ba su damar komawa gidajensu don yin noman doya da sauran kayan gona.

Bayanan da Aminiya ta samo sun nuna cewa, manoman na cikin zullumi da damuwar komawa garuruwansu don yin noma, duk da yarje musu da ’yan ta’addan suka yi bisa la’akari da abin da ya faru a bara, bayan ’yan bindigar sun bar su sun yi noma, amma kwashe kayan gona ya gagara saboda hare-hare musamman a yankin Chukuba da sauran kauyukan da ke wurin.

Wani manomi a kauyen Chukuba ya ce, manoman yankin sun fara komawa gida don yin noma bayan ’yan ta’addan sun yarje musu, “Amma babban tsoronmu shi ne tuna abin da ya faru a bara, inda bayan an gama noma da lokacin girbi ya yi suka hana mu cire amfanin gona haka doya da sauran kayan gonar da muka shuka muna ji muna gani muka yi asararsu. Irin wannan kasadar muka sake jefa kanmu a ciki yanzu,” inji shi.

Sai dai yayin da manoman yankin Chukuba ke iya komawa don yin noma, su kuwa manoman garuruwan Kuchi da Injita da Chibani da Zazzaga da wasu garuruwan Karamar Hukumar Munya sun ce, har yanzu ba su samu damar komawa gona ba saboda hareharen da ake kai wa kauyukansu.

Wani dan gudun hijira daga garin Kuchi mai suna Mohammad Awwal, ya ce duk lokacin da suka koma gida don yin noma sai an kai musu hari, an kama wadansu daga cikinsu.

Bana ba mu yi noman doya ba duk da muna dada shiga damina. Ya kamata a ce yanzu mun gama dashen doya domin farkon damina ne lokaci mafi dacewa da shuka doya,” inji shi.

A cewarsa, “A garuruwanmu ’yan ta’addan suke zama. Wadansu ’yan uwanmu sun shaida mana cewa, sun bar doyar tamu a bude tare da awakin da muka bari suna ta cinye irin doyar da muka baro a can.”

Shi ma wani manomin mai suna Shehu Abubakar, ya ce mutane kadan ne suke kasadar zuwa noma abin da ya samu na kayan gona kuma cikin fargaba.

Ya ce, ba sa zuwa gona da yara da mata a yanzu saboda gudun kawo hari sabanin yadda suke yi a baya, inda yara da mata ke zuwa don taya iyaye da mazansu aiki a gona.

“Yanzu hekta nawa ne manomi daya zai iya nomawa? Ka ga babu wani noman kirki da ake yi a yankin. Kai, in takaita maka zance kusan kashi 90 cikin 100 na kauyukan Karamar Hukumar Munya, babu kowa a cikinsu ka ga babu maganar wani noman kirki da za a yi a Munya,” inji shi.

Wani manomi a kauyen Gwada da ke Karamar Hukumar Shiroro ya ce, matsalar tsaro ta shafi gonaki da dama a yankunan kananan hukumomin Shiroro da Munya saboda babu wanda zai sayar da rayuwarsa da sunan zuwa gona.

Yayin da ayyukan ta’addanci suke ci gaba da gudana a kananan hukumomin biyu, inda ake jefa manoma cikin tasku, da yawan manoman sun yi hasashen samun karancin doya da sauran kayan abinci a shekarun nan matukar gwamnati ba ta dauki tsauraran matakai a kan ’yan ta’addar ba, ta yadda manoma za su samu damar komawa garuruwansu don ci gaba da noman.

Amma Sakataren Kungiyar Masu Sayar da Doya ta Babbar Kasuwar Paiko, Malam Abubakar Hussaini, ya ce a yanzu manoma sun fara noman doya.

“Hatta wadanda ba su samu damar yin noma a bara ba, sun fara noma a bana. Duk da cewa da yawansu na zuwa gonan cikin firgici da tsoro, abin da suke yi shi ne suna barin mutum biyu zuwa uku domin yin gadinsu, inda da zarar sun hango maharan sai su sanar da ’yan uwansu domin su gudu,” inji shi.

Ya ce, a bana manoman na samun zuwa gonakinsu sabanin shekarun baya saboda samun ci gaba a harkar tsaro. Shugaban ya ce, babban kalubalen da suke samu a bana shi ne, irin doyar ya yi tsada saboda rashin noma sa a bara da kuma rashin samun damar zuwa ciro ta ga wadanda suka noma.

Malam Hussaini, ya kara da cewa, “Manoma daga Munya da Shiroro suna zuwa sayen irin doya a wajenmu. Irin da muke sayarwa a kan Naira dubu 10 a bara, a bana ana sai da shi ne a kan Naira dubu 40 saboda karancinsa da kuma karuwar bukatarsa.”

Ya ce, “Da yawan manoma ba su iya noma doya fiye da hekta daya ba, saboda tsada domin noma hektoci na bukatar kudi mai yawa. Irin doya guda 100 ana sayar da shi ne a kan Naira dubu 20 kuma hekta daya na bukatar iri 300.

“Shekarun da suka wuce manoman sun noma fiye da hekta 10, amma ba su iya cirewa ba.”

Ya yi kira ga gwamnati ta dauki tsauraran matakai don shawo kan matsalar tsaro ta yadda manoma za su samu damar komawa kauyuka da garuruwansu don ci gaba da rayuwa.

Ya ce mafi yawansu ba su da wata hanya ta dogaro da kai da ta wuce noma.