✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Manyan Arewa da ke cikin gwamnatin Jonathan ba su taimaka mata’

Tsohon Shugaban Matasan rusasshiyar Jam’iyyar NPP a Jihar Filato Alhaji Haruna Usman ya ce Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Muhammad Namadi Sambo da sauran jami’an gwamnatin…

Tsohon Shugaban Matasan rusasshiyar Jam’iyyar NPP a Jihar Filato Alhaji Haruna Usman ya ce Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Muhammad Namadi Sambo da sauran jami’an gwamnatin Jonathan ’yan Arewa ba su taimaka wa Arewa ba balle su nuna damuwa kan halin da take
ciki.
Alhaji Haruna Usman ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos don mayar da martani kan maganganun da Alhaji Namadi Sambo ya yi a kwanakin baya a fadar Sarkin Kano.
Alhaji Haruna Usman ya ce maganganun da Alhaji Namadi Sambo ya yi a fadar inda ya ambaci sunayen Ministan Tsaro Janar Aliyu Gusau da Shugaban ’Yan sandan Najeriya Alhaji Sulaiman Abba da Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki da shi kansa da suke cikin gwamnatin Goodluck Jonathan ba za su yarda a ci mutuncin Arewa ba, domin su ’yan Arewa ne masu kishin Arewa.
Alhaji Haruna ya ce duk kashe-kashen da ake yi a Arewa, Mataimakin Shugaban kasa bai taba fitowa ya nuna damuwarsa ba, ta hanyar fitowa ya yi magana.
Ya ce a kwanan baya Alhaji Sulieman Abba, ya sa aka hana dan uwansa dan Arewa Shugaban
Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal shiga majalisar kuma da aka kira shi gaban majalisar ya ce shi bai yarda Tambuwal ne shugaban Majalisar Tarayya ba.
Ya ce a kwanakin baya da aka kama jirgin shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya a Afirka ta Kudu dauke da makudan kudi za a je a sayo makamai, Sambo Dasuki da kansa ya fito kare wannan al’amari.
Alhaji Haruna Usman ya ce a lokacin da aka nada Janar Aliyu Gusau a matsayin Ministan Tsaro ya kiro shugabannin rundunonin sojin Najeriya, domin ya tattauna da su kan matsalar tsaro a Arewa suka ki zuwa, amma bai sauka daga kan mukaminsa ba, “wadannan abubuwa da wadannan jami’ai suke yi ne kishin Arewa da kare ta?,” inji shi.
Ya yi kira ga al’ummar Arewa su ci gaba da yin addu’o’in Allah Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa.