✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marasa lafiya 500 sun samu tallafi a Kaduna

Marasa lafiya sama da 500 ne suka amfana da tallafin magani kyauta da dan takarar Majalisar Wakilai, Ali Mu’azu ya dauki nauyi a Karamar Hukumar…

Marasa lafiya sama da 500 ne suka amfana da tallafin magani kyauta da dan takarar Majalisar Wakilai, Ali Mu’azu ya dauki nauyi a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa.

Marasa lafiyan wadanda akasarinsu talakawa ne, an ba su maganin cututtukan da suka hada da ciwon ido da kaba da sauransu. Wadansu kuma an ba su gilasan ido ne, wadansu kuma aiki aka yi musu a kyauta.

A cewar wanda ya shirya ba da maganin kyauta, ya yi haka ne domin taimaka wa talakawan yankinsa domin akasarinsu masu karamin karfi ne.

Ya bayyana haka ne ta bakin daraktan yakin neman zabensa, Haruna Ali Zanna a lokacin da yake zantawa da Aminiya jim kadan da kaddamar da shirin a asibitin PHC da ke Badawara Kaduna.

Ya ce akasarin wadanda suka amfana da wannan shiri ba ’yan jam’iyya daya ba ne, mutanen Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa da kuma sauran unguwanni sun  amfana.

“Wannan shiri na kowa da kowa ne, babu ruwanmu da siyasa domin idan ka duba, talakawa ne marasa karfi ake taimaka wa saboda Ali Mu’azu ya fahimci cewa al’umma na cikin halin rashi kuma dama abin alheri ne da ya dade yana yi,” inji Zanna.

Ya nemi jama’a su zabi cancanta a zabe mai zuwa, wadanda za su taimaka musu ko bayan sun ci zabe.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban Jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Mohammed Hamisu Dantajiri, cewa ya yi aikin alheri abu ne da jam’iyyarsa ta saba yi ga jama’a. Don haka sai ya gode wa dan takararsu Ali Mu’azu bisa hangen nesarsa na ganin ya taimaka wa talakawan yankinsa.