✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marigayi Bashir Musa Liman: Irin  rashi da muka yi!

Kasancewata ma’abocin bibiyar kafar sadarwa ta Instagram inda marigayin Bashir Musa Liman ke taba alamar “like” na hotunan da nake sakawa. Irin bibiyar ce ta…

Kasancewata ma’abocin bibiyar kafar sadarwa ta Instagram inda marigayin Bashir Musa Liman ke taba alamar “like” na hotunan da nake sakawa. Irin bibiyar ce ta sa na ci karo da bugun zuciyata matuka da tsai da tunani tare kuma da dimuwa bayan da jarumar fina-finan Hausa Hadiza Aliyu Gabon ta saki muryar mamacin a shafinta yana wa’azin cewa duk abin da ke akwai a duniya sai ya kare kuma sai ya tafi kamar ba a yi shi ba. A kasa ta rubuta tarji’i ta bayyana mutumin kirki ne shi.

Sai na fara kokarin binciken kusa na wadanda suke tarayya da na sani, na yi ta faman kiran wayar Darakta Kamal Alkali ta ki shiga, na tambayi Isah Bawa Doro ya ce bai sani ba shi ma gaskiya, amma ya ba ni shawarar in kira wayarsa kai-tsaye. Na kira ne da niyyar jin murya mai fara’a da barkwanci da ilimi matuka, amma ba da son raina ba na ji wata murya mai karfin hali amma da damuwa karara a cikinta ta wani bawan Allah da ban tsaya tambayar sunansa ba ya ce min “Malam mai wayar nan Allah Ya yi masa rasuwa, ya yi hadarin mota ne!” Na san Ubangiji Ya halicce shi kuma Shi Ya karbe abinSa amma sai na ji maganar kamar babu ita. Saboda haka sai na kara hawa shafin inda na ga ana saka hotonsa na ban-kwana da sanar da rasuwarsa har da turakarsa ta Facebook. Daga nan ne na gane ashe an kai awa hudu da rasuwar tasa.

Akwai abubuwa da dama da suke da alaka da rayuwarsa da suka zamar min darasi da ilimi tare da samun nasara. Idan har Bashir ya tabbata za ka iya abu, na daya zai yi maka gyara ya nuna maka ka ci gaba da yi da shawarwari masu kyau. Ya kyankyashe wani matashi Nasiru Tanimu Annuri har ya kai ga tudun-mun-tsira ta hanyar aikin jaridar dab’i. Tare kuma da ni duk da harshen Hausa na karanta amma yana min gyararraki ta hanyar wayar salula da kuma dora ni bisa gwadaben yin aiki tukuru da jajircewa. Duk wadannan ba su ne dalilan da suka sanya na fara alaka da shi ba, rubutunsa kafin jaridar Aminiya ta dauke shi aiki shi ne dalilin haduwarmu.

Yana yin rubutu kan addini kamar sheihi fiye da tunanin mutane, a lokaci guda kuma zai iya yi maka sharhi na musamman kan kwallon kafa a kasa da kuma Turai da harkokin fina-finai kamar shi ya kirkire su. Yana rubutu kan soyayya da zamantakewa, ban manta da wani rubutu da ya yi ba kan magungunan kayan da’a da mata ke amfani da su ba, da ya nuna illolinsu; inda za a gane ya ci sunan kibdau dinsa na ‘Diddigi’ domin gwanin bincike ne matuka.

Wani sirri da ke tsakaninmu da ya taba fada min shi ne batun daukarsa aiki, saboda ina da bukatar karanta rubutunsa a koyaushe. Makon da aka tabbatar masa ya fada min ya ce in yi shiru don ba kowa ya sani ba, na ji dadi sosai matuka. Shi ya sa a shekarar 2015 na ziyarce shi har babban ofishin Daily Trust da ke Abuja muka yi zumunci kuma ita ce haduwata ta farko da shi kuma ta karshe a duniya, domin sai mun yi za mu hadu saboda yanayin aiki sai kowa hidimarsa ta hana.

Daga baya-bayan nan abubuwan da zan iya tunawa su ne, kokarin da ya so ya yi na in rika yi wa wata jarida rubutu ana biyana. Ayyuka sun yi min yawa amma saboda kaunar da nake masa ya sanya na amince, maganar da ba mu ida ba. Sai kuma wani shirin bidiyo na Kamal S. Alkali da ya hada mu ya kai masa sunana don yin aiki a tare.

Ba mu taba samun sabani ma ko jin assha game da shi ba, masanin harshen Ingilishi ne kuma masanin ilimin duwatsu (ma’adanai) wanda ya karanta a jami’a, sannan mai yawan sako labaran gaskiya kuma da dumi-duminsu a lokacin da ake bukata, garkuwan labaran ’yan masana’antar Kannywood.

Dalilin ilimin duwatsun ne ya sa yake aiki a Jos kafin rasuwarsa, amma da yake kwakwalwarsa mai kyau ce kai ka ce aikin jaridar ne ya karanta. Duk tambayar da za ka yi masa sai ka ji kamar ya rubuta ne yake ba ka amsa cikin natsuwa sosai.

A cikin ban-kwanansa da duniya a ’yan kwanaki kafin rasuwarsa wa’azi ne mai ratsa jiki game da duniya da mutuwa da kuma Lahira. Tsarki ya tabbata ga Ubangiji. Ga abin ya fada da cikin harshen Ingilishi ni kuma na fassara da Hausa a cikin dakika 36 a Whatsapp:

“Sunana Bashir Liman, zan ba ku shawarwari a kyauta. A wannan duniyar babu abin da zai dore har abada tun daga kan mulki da kudi da kadarori da kyau duk sai sun gushe sai dai ayyukanka kadai.

Idan ka yi nagari ka samu sakamako mai kyau haka ma idan ka yi na banza. Na kirki su kai ka Aljanna, na banza kuma wuta, ka gina duniyarka da ayyuka nagari domin Lahirarka ta yi kyau ka samu farin ciki.”

Allah Ubangiji Ya jikansa da rahama Ya gafarta masa Ya yafe masa Ya yalwata makwancinsa da ni’imomi dauwamammu har ranar tsayuwa da za mu tashi a gaban Ubangiji don karbar sakamako, amin.

Kabir Sa’idu Bahaushe Dandagoro (08038387516)

Dan jarida ne a gidan Rediyon Bision FM  a Katsina Jihar Katsina.