✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Masar ba za ta sa baki kan shari’ar ‘yan jaridan Aljazeera ba’

Shugaban kasar Masar Abdulfattah el-Sisi ya ce ba zai tsoma baki akan hukuncin da aka yanke wa ’yan jarida Aljazeera ba.A ranar Litinin ne dai…

Shugaban kasar Masar Abdulfattah el-Sisi ya ce ba zai tsoma baki akan hukuncin da aka yanke wa ’yan jarida Aljazeera ba.
A ranar Litinin ne dai wata kotu a birnin  Alkahira  ta yanke wa wasu ’yan jaridar  Aljazeera uku hukunci daurin shekara bakwai, wanda hakan ya janyo  kalaman Allah-wadai daga kasashen duniya da dama.   Kotun ta same ’yan jarida uku wato: Peter Greste da Muhammad Fahmy da kuma Baher Mohammad da laifin yada labarai karya. Amma ’yan jaridar sun musanta zargin kuma sun ce za su daukaka kara.
Ministan Harkokin Wajen kasar Australiya Julie Bishop ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa  kasarsa za ta yi dukkannin mai yuhuwa don ganin an sallami daya daga cikin ’yan jaridar wanda dan kasar ta Australiya ne.
A ranar Talatar da ta gabata wasu jama’a a birnin Landan sun yi wani gangami da ke bayyana bukatar sako dukkannin ’yan jaridar ba tare da wani bata lokaci ba.
An kama ’yan jaridar ne a ranar 29 ga watan Disambar da ya gabata kuma a yanzu ana tsare da su ne awani gidan yarin Tora na birnin Alkahira.