✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Kano ta dakatar da dagaci kan yi wa yarinya fyade

Masarautar Kano ta bayar da sanarwar dakatar da Dagacin garin Goron Maje a karamar Hukumar danbatta da ke Jihar Kano bisa zarginsa da yi wa…

Masarautar Kano ta bayar da sanarwar dakatar da Dagacin garin Goron Maje a karamar Hukumar danbatta da ke Jihar Kano bisa zarginsa da yi wa wata yarinya mai kimanin shekara 14 fyade tare da sanya mata cutar kanjamau.
Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi ne ya bayar da sanarwar dakatar da Dagacin inda ya ce bayan dakatar da Dagacin da masarautar ta yi ta kuma tura maganar gaban Hukumar Hisba tare da kafa kakkarfan kwamiti don bincikar gaskiyar lamarin.
Aminiya ta samu labarin cewa asirin Dagacin ya tonu ne lokacin da aka kai yarinyar da wanda zai aure ta (an sakaye sunayensu) asibiti don a yi musu gwajin cutar kanjamau, a nan ne aka same ta da kwayar cutar yayin da wanda zai aure ta ba ya da ita.
kanen mahaifin yarinyar, Malam Muhammad Tukur ya bayyana cewa samun wannan sakamako daga asibiti ne, “Ya sa muka takura wa yarinyar da bincike a nan ta sanar da mu cewa Dagaci ne yake nemanta a lokacin da take daukar talla. A cewarta Dagacin ya yi mata barazanar zai yanka ta idan har ta gaya wa wani halin da ake ciki,” inji shi.
Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wa Aminiya cewa bayan masarautar Kano ta tura musu matsalar sun gayyaci Dagacin na Goron Maje inda aka yi masa gwajin cutar kanjamau aka kuma same shi da cutar tare da shi.
Sheikh Aminu Daurawa ya yi kira ga iyaye su rika kula da shige da ficen ’ya’yansu, domin gudun fadawa hannun miyagun mutane. Sheikh Daurawa ya kara da cewa, “A yanzu haka masarautar Kano ta ba mu umarni za mu yi aiki tare da kwamitin da ta kafa don ci gaba da bincike kan gaskiyar lamarin. Muna kira ga iyaye su rika kula da tarbiyyar ’ya’yansu tare da sanya idanu a kan ’ya’yan don gano duk wani canji da ka iya aukuwa gare su a dauki matakin da ya dace a kan lokaci.”