✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Zazzau: Lauyan Iyan Zazzau ya janye kara

Lauyan marigayi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN ya janye karar da suka shigar ta kalubalantar nadin Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a…

Lauyan marigayi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN ya janye karar da suka shigar ta kalubalantar nadin Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau.

Hakan na zuwa ne bayan rasuwar Iyan Zazzau wanda ya koma ga Mahaliccinsa a ranar 1 ga Janairu, 2021.

Lauyan ya ce, “A ka’ida ranar Laraba za mu shiga kotu don ci gaba da sauraron shari’a, sai dai Allah ya yi wa Iyan Zazzau rasuwa, ranar 1 ga Janairu, 2021 a jihar Legas.

“Wannan shari’a ba irin wadda wasu za su gaje ta bane, don haka ba mu da wani zabi face mu janye karar, tunda wanda ya shigar da ita ya rasu,” cewar Ustaz.

“Kuma saboda mun kira irin wannan shari’ar ta sirri tunda ba kamar shari’ar ba ce cewa magada za su iya shiga cikin takalmin fatar.

“Irin wannan shari’a tana mutuwa ne tare da wanda ya shigar da ita kamar yadda doka ta bayar da zabi don haka ba mu da wani zabi da ya wuce janye karar.

“Don haka muka nemi a janye karar kuma kotu ta amsa bukatarmu.

Kafin rasuwarsa, Iyan Zazzau ya shigar da kara kotu inda ya ke kalubalantar gwamnatin jihar Kaduna kan nada Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19, bayan rasuwar marigayi Shehu Idris a ranar 20 ga Satumba, 2020.