✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan aure 30 sun haddace Alkur’ani Mai girma a Gombe

Makarantar Islamiyya ta Al-Burhan da ke Gombe ta yi bikin saukar karataun matan aure 30 da suka haddace Alkur’ani Mai girma. Da yake jawabi a…

Makarantar Islamiyya ta Al-Burhan da ke Gombe ta yi bikin saukar karataun matan aure 30 da suka haddace Alkur’ani Mai girma.

Da yake jawabi a wajen taron Mataimakin Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Usman Isa Taliyawa, ya jawo hankalin masu hannu da shuni  kan taimaka wa karatun ’ya’yan marasa galihu. Ya kuma yi kira ga iyaye su rika sanya ido kan karatun ’ya’yansu, sannan ya ce ya fi kyau iyaye su sayar da kadarorinsu wajen karatun ’ya’ya a kan su sayar don yi musu aure.

Ya ce ilimi shi ne hasken rayuwa kuma shi ne hanyar tsira, “Domin idan ba ka yi ilimi ba ta yaya za a yi ka san yadda za ka bauta wa Allah?” Ya yi tambaya.

Sheikh Adamu Muhammad Umar, taya wadanda suka haddace Alkur’anin murna ya yi, inda ya ce duk wanda ya haddace Alkur’ani zai cece shi a ranar gobe. Ya ce Manzon Allah ya ce duk wanda ya haddace Alkur’ani yana da waje na musamman a gidan Aljanna.

Sai ya shawarce su da su koyi fassarar Alkur’ani tunda sun haddace shi, don sanin ma’anarsa. Ya kuma yi amfani da wannan dama ya yi kira ga gwamnati da ta sanya makarantun Islamyya a tsarin karatu na zamani, ta yadda idan mutum ya canja gari zai iya yin komawa karatunsa inda ya sauka, sauran makarantun gwamnati, ba sai mutum ya sake daga farko ba.

Shi ma Shugaban Kungiyar Izala ta Jihar Gombe Injiniya Salisu Muhammad Gombe, cewa ya yi wannan sashi na mata da aka bullo da shi a shekarar 2012, ya taimaka domin mata da yawa sun samu dama sun yi karatu. Ya gode wa Daraktan Makarantar Malam Ahmad Musa bisa jajircewarsa wajen ciyar da ilimi gaba. Daga nan sai ya yi kira ga ’yan Najeriya su sadaukar da kansu wajen yi wa kasar nan addu’o’i don yin zabe cikin lumana.

Daraktan Makarantar Malam Ahmed Musa, bayyana jin dadinsa ya yi na yadda ya samu hadin kan jagororin makarantar, wanda da hakan ne makarantar ta ci gaba.

Wadansu mata da suka haddace Alkur’anin sun bayyana cewa wannan makaranta ta yi musu komai, domin ta dalilinta ne suka samu damar haddace Alkur’ani.