✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsin lamba ba zai sa ni barin mulki ba – Assad

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban Siriya Bashar al-Assad, ya ce ba zai sauka daga kan mulki ba saboda matsain lambar kasashen Yamma, sai dai idan…

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban Siriya Bashar al-Assad, ya ce ba zai sauka daga kan mulki ba saboda matsain lambar kasashen Yamma, sai dai idan ‘yan kasar ne suka ce ba su yarda ya ci gaba da mulkin ba, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
A lokacin da Shugaba Assad ya ke yiwa manema labaran Rasha jawabi ya ce tururuwar da ‘yan Siriya suke yi zuwa kasashen nahiyar Turai na faruwa ne saboda ‘yan gudun hijirar suna gudun ta’addanci, amma ba gwamnatinsa ba.
Shugaba Assad ya yi wannan jawabin ne kwana guda bayan Shugaba bladimir Putin na Rasha ya bukaci sauran kasashe su bi sawun kasarsa wajen goyon bayan gwamantin Shugaba Assad.
Sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry, ya ce idan Rasha ta ci gaba da mara wa shugaban baya, akwai hadarin rikicin kasar zai kara daukar tsawon lokaci kafin a shawo kansa.
Rikicin kasar wanda ya fara a watan Maris din shekarar 2011, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma tilasta wa wasu barin muhallinsu.