✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matukin jirgi

Wani matukin jirgi ne ya dauki wasu mahaukata a cikin jirgin sama, daya daga cikinsu kuwa yana kusa da shi a yayin da yake tuka…

Wani matukin jirgi ne ya dauki wasu mahaukata a cikin jirgin sama, daya daga cikinsu kuwa yana kusa da shi a yayin da yake tuka su. Shi wannan mahaukaci, ana tsammanin ya kusa warkewa, ya fi sauran hankali. Suna tsakar tafiya, sai sauran mahaukatan suka yi ta kara da surutu mai yawa. Ganin haka sai matukin jirgin ya ce wa wanda ya kusa warkewa: “Ka je ka tsawata musu, su daina surutu, sun dame mu haka nan.” Shi kuwa ya amsa, ya tashi ya tafi. Jim kadan sai ga shi ya dawo ya zauna, ya ce: “Haba, ka ji wurin duk ya yi tsit!” Da direba ya tambaye shi dalili, sai ya ce: “Ai da na ce musu su yi shiru suka kiya, sai na bude kofar jirgin nan, na ce duk wanda ba zai shiru ba ya fita. Shi ne suka yi ta fita daya bayan daya har suka kare!”
Daga Shehu Lawal Tsafe 08091573703