✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mauludi: ‘Bana mun dauki mataki kan matasa batagari a ranar jerin gwano’

A shirye-shiryen da Shugabanin Kungiyar Makarantu Islamiyya suke yi a Gombe don bikin murnar zagayowar Ranar Haihuwar Fiyayyen Halitta Annabin Rahama (SAW), Shugaban Kungiyar Alhaji…

A shirye-shiryen da Shugabanin Kungiyar Makarantu Islamiyya suke yi a Gombe don bikin murnar zagayowar Ranar Haihuwar Fiyayyen Halitta Annabin Rahama (SAW), Shugaban Kungiyar Alhaji Muhammad Nuhu ya ce sun shirya daukar mataki kan batagarin da suke sa matattun kaya a jikinsu  inda suke haifar da matsala a wannan rana.

Bikin da za a yi a ranar Litinin 11 ga watan nan na Nuwamba, Alhaji Muhammad Nuhu ya ce duk wanda suka kama da irin wannan shiga ko ya dauki sanda ko wani makami a hannunsa za su hada shi da hukuma domin ba masoyin Annabi ba ne.

Alhaji Muhammad Nuhu ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa a Gombe inda ya ce an tsara yadda dukkan ’yan makarantun Islamiyya za su bi idan suka fito cikin tsari ba tare da hayaniya ba.

A cewarsa sun samu hadin kan dukkan bangarorin jami’an tsaro don shawo kan duk wata barna da za ta taso.

Alhaji Muhammad Nuhu ya kara da cewa sun dauki matakin hana masu shigar banza da suke sa tsummokara su rataya katon carbi suna shiga irin ta hauka suna shiga cikin jerin gwano don bata musu suna da jawo musu zagi.

Ya ce idan suka kama mutum cikin irin wannan shigar za su kai shi kotu, don ya ci mutuncin masoyan Annabi (SAW) a ranar da suke bikin murnar zagayowar haiwuwarsa.

Shugaban Kungiyar Makarantun ya ce a wannan karo suna sa ran dukkan kananan hukumomin jihar 11 za su shigo cikin garin Gombe don wannan biki.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati ta shigo wajen tallafa musu daukar nauyin gudanar da shirye-shiryen a kafafen watsa labarai don sakon ya kai ko’ina.