✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawaka mu rika amfani da kalamai masu kyau – Lil-Teemarh

Aminiya: Za mu so mu sanin takaitaccen tarihin rayuwarki? Lil-teemarh: An haife ni a unguwar Goron Dutse a Jihar Kano. Na yi karatun firimary dina…

Aminiya: Za mu so mu sanin takaitaccen tarihin rayuwarki?

Lil-teemarh: An haife ni a unguwar Goron Dutse a Jihar Kano. Na yi karatun firimary dina a Nasiha Academy da ke Janbulo. Bayan na gama sai na tafi makaranatar Sakandire ta El-Buhaj Academy. A yanzu haka na kammala ina kuma karatu a Makarantar School of Health Technology da ke Kano a bangaren binciken cututtuka wato Lab science. 

Aminiya: Ya aka yi kika fara harkar waka?

Lil-teemarh: Eh to, Ni dai kawai na tashi na samu kaina a harkar waka ne. Tun ina karama. wanda zan iya cewa tun ina matakin karatun Nursery nake waka. Lokacin da na shiga Firamare sannan na fara rubuta waka, amma ban fara zuwa dakin raira waka ba wato studio sai da na shiga Sakandare. Ina aji daya a Sakandare na fara shiga studiyo ina raira waka a shekarar 2009 ke nan. 

Aminiya: Kasancewarki yar  makaranta ya kike hada waka da karatu?

Lil-teemah: Nakan ajiye yin waka lokacin makaranta, kamar idan ina da lacca ranar da zan yi waka; to in sha Allah nakan ajiye yin waka sai bayan na tashi daga makaranta, idan ya kasance dole sai a ranakun aiki za a yi wakar ke nan. Sai dai ma ni na fi yin waka a lokacin hutun karshen mako, nakan gaya wa duk wanda zan fito a wakarsa cewa ya yi hakuri ya bari har sai ranar Asabar ko Lahadi.  Ina mayar da hankalina sosai a kan karatuna saboda na san muhimamncin karatun. 

Aminiya: Lokacin da kika fara waka ya iyayenki suka karbi lamarin, duba da yanayin wurin da kika taso a cikin birni Kano?

Lil-teeemarh: Gaskiya na sha wahala matuka da farko, ba wai ma fara yin salon wakar hip-pop din kawai ba, tun farkon fara yin wakar gaba daya ba su so ba. Suna tunanin idan na fara harkar waka zan sauka daga tarbiyyar da suka ba ni, ko kuma zan guji makaranta. Daga karshe da suka gane sai suka zo suna ba ni goyan baya, tunda sun fuskancin inda na sa gaba. A yanzu har sauraron wakokina suke yi. Kamar wakar da na yi mai suna Jauro ina dan sanya kalmomin Fulatanci a ciki, to wannan kalmomi mahaifina ne ya taimaka min da su. Haka kuma ita ma mahaifiyata ta taimaka min da wasu kalmomin a cikin wakata ta ’yar makaranta haka su ma matan babana suna taimaka min wajen ganin na yi wakokina. 

Aminiya: Mene ne jigon wakokinki ko a kan me kika fi waka?

Lil-teemarh: Babu bangaren da ba na yin waka, nakan fadakar  haka kuma nakan nishadantar.  Amma yawancin wakokina na fadakarwa ne. misali idan ka dauki wakata ta rayuwa inda na bayar da labari a kan wani saurayi da ke da kudi, amma ya bar gida ya ki ’yan uwansa, ya tafi kasar waje yana ta shashancinsa. Daga karshe sai ya zamana ba shi da kudin kullum sai dai ya je wajen abokansa su ba shi, har ta kai a karshe suna wulakanta shi. Ita kuma dayar macen irin tarbiyar da iyayenta suke yi mata take ganin kamar sun takura mata, daga karshe ta bar gidansu takoma waje tana shaye-shaye da sauransu, ta samu kudi amma daga karshe kudin suka kare sakamakon gobara da ta yi a karshe dai har bara ta fara yi. Haka kuma idan kika dauki wakata ta ’yar makaranta  inda ta hau mota aka rage mata hanya, wanda ya dauke ta a karshe ya kai ta gidan yankan kai. Haka kuma na fi yin amfani da salon rapping  na Hausa kawai. Koda yake wani lokacin nakan sa Turanci, amma gaskiya na fi yin na Hausa. 

Aminiya: Shin wakoki nawa kika yi kuma kin taba yin albam na gani ko na saurare?

Lil-teemarh: A yanzu haka ina da waka goma wanda duk an buga su, na fitar da biyar daga cikinsu kamar ‘yar makaranta da jauro da I need you da labari, sai wata kuma da ake cewa Jummai mai koko. Sai dai gaskiya har yanzu ban yi kundi ba wato albam, amma insha Allah ina sa ran zan yi na bidiyo  kwanan nan. 

Aminiya: Ana zarginku mawaka da rashin hadin kai meke kawo hakan, laifin na manyana mawaka ne ko kuma naku ne mawaka masu tasowa? 

Lil-teemarh: Gaskiya zan iya cewa daga manyan mawaka ne. Alal misali a matsayina na mawakiya mai tasowa idan ina so na ga wani babban mawaki sai na sha wahala. Ko kuma idan na ce yau ina so zan yi waka da wani babban mawaki to kudin da zai nema na ba shi ya yi yawa sosai wanda bazan iya biya ba. Gaskiya zan iya cewa akwai tazara tsakaninmu, idan ban da Alhamdulillah zan iya cewa Billy o da yake wani shiri a gidan Rediyon Dala FM yake gayyatar mawaka masu tasowa irinmu, da kuma Nomis Gee da yake shiri a gidan talabijin na AREWA 24 inda yake tallata mawaka irinmu, to da babu wanda ma zai san da mu. 

Aminiya: Wane kira kike da shi ga ‘yan uwanki mawaka don ganin an kara inganta harkar waka?

Lil-teemarh: Kirana ga ’yan uwana mawaka  shi ne su yi hakuri, domin duk abin da hakuri bai ba ka ba, to rashinsa bazai baka ba, idan kai hakuri komai zai zo gareka sai dai wataran ka bayar da labari. Haka kuma akwai bukatar mu mawaka mu rika yin amfani da kalamai masu kyau a cikin wakokinmu duba da dimbin jama’ar da ke sauraron wakokin, wanda mafi yawansu matasan ne, don gudun kada a lalata tarbiyyar matasanmu. 

Aminiya: Shin kuna samun tallafi daga bangaren gwamnati?

Lil-teemarh: Gaskiya ba mu samun tallafi daga gwamnati, wanda kuma muna bukata kwarai da gaske. Misali idan muna so mu yi album ba mu da kudi ko kuma muna tunani idan mun yi kundi (album) wa zai saya, su ‘yan kasuwa suna gani kamar shirme ne ba za su sa kudinsu su saya ba. Ina kira ga gwamnati ta samu ta zauna ta ga irin  sakon da mu mawaka muke da shi wanda kuma yake zama ci gaba ga al’umma sai ta ga irin tallafin da ya dace ta ba mu. 

Aminiya: Wani sako kike dashi ga masoyanki?

Lil-teemarh: Na san burin masoyana shi ne su ga na fara bidiyo kuma insha Allah ina nan ina shiri a cikin sabuwar shekarar nan ta 2018 zan gama insha Allah.