✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawakiya Di’ja ta fara fitowa a fim

Fitacciyar mawakiyar nan Hadiza Blel, wadda aka fi sani da Di’ja ta fara fitowa a fim din Kannywood. Ta fito ne a fim din Mati…

Fitacciyar mawakiyar nan Hadiza Blel, wadda aka fi sani da Di’ja ta fara fitowa a fim din Kannywood.

Ta fito ne a fim din Mati a Zazzau da mutane suka dade suna tsimayinsa,  ganin cewa ya zo da sabon salo, ciki har da kasancewar sabuwar jaruma wato mawakiyar wadda ta fi karewa a bangaren wakokin R&B.

It dai Di’Ja mahaifiyarta ’yar Arewa ce, mahaifinta kuma asalinsa dan kasar Saliyo ne.

Kamfanin Sadau Pictures Production ne ya shirya fim din, kuma Rahama Sadau da Sadik Sani Sadik suka dauki nauyi, sannan Yaseen Auwal ya bada umarni.

Akwai jarumai irin su Adam A. Zango da Rahama Sadau da Sadik Sani Sadik a cikin shirin wanda za a fara haskawa a sinima a watan Fabrairu.