✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayaka sun kashe alkalin da ya yanke wa Saddam Hussein hukuncin kisa

Mayakan kungiyar ISIS sun kashe alkalin da ya yanke wa tsohon Shugaban kasar Iraki Saddam Hussein hukuncin kisa. Bayanai sun ce ’yan bindigar sun kashe…

Mayakan kungiyar ISIS sun kashe alkalin da ya yanke wa tsohon Shugaban kasar Iraki Saddam Hussein hukuncin kisa. Bayanai sun ce ’yan bindigar sun kashe Alkali Raouf Abdul Rahman da ya yanke hukuncin ratayewa ga Saddam a shekarar 2006 don daukar fansar kashe Saddam mai shekara 69.
Gwamnatin Iraki ba ta tabbatar da labarin ba, kuma jami’an gwamnati ba su musanta rahoton kama shi a makon jiya ba. Ana da yakinin an kama shi ne a ranar 16 ga Yuni, kuma aka kashe shi bayan kwana biyu.
Wani dan majalisar dokokin Jordan, Khalil Attieh ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa Alkali Rahman da ya jagoranci Kotun kolin da ta yi wa Saddam shari’a, ya shiga hannu kuma an kashe shi.
“Masu ra’ayin juyin juya-hali sun kama shi, kuma sun yanke masa hukuncin kisa don daukar fansar kisar shahidi Saddam Hussein,” inji shi, kamar yadda jaridar Al-Mesyroon ta ruwaito.
Attieh ya ce Alkali Rahman ya yi yunkurin ya gudu daga Baghdad ta hanyar shiga irin ta masu rawa.
Shafin Facebook na Izzat Ibrahim al-Douri, tsohon Mataimakin Saddam wanda jigon mayakan Sunni ne ya rubuta cewa mayakan sun samu nasarar kama Alkali Rahman.
Akali Rahman mahaifin ’ya’ya uku ya kammala karatun shari’a a Jami’ar Baghdad a 1963, kuma ya yi aikin lauya kafin nada shi Babban Alkalin Kotun daukaka kara ta Kurdistan a 1996.
Ya jagoranci shari’ar zargin Saddam kan kisan mutum 148 a garin Dujail bayan yunkurin kashe shi a 1982, kuma ya yanke masa hukuncin ratayewa.
An rataye Saddam ne a ranar da Musulmi Sunni ke bukukuwan Babbar Sallah, kuma bidiyon rataye shi ya nuna yadda ’yan Shi’a suka rika tozarta shi.
Alkali Rahman daga baya ya soki yadda aka aiwatar da hukuncin rataye Saddam a gaban wasu jama’a, inda ya ce bai kamata a aikata haka a wannan zamani ba.