✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan IS sun harbo jirgi a Siriya

Mayakan kungiyar kafa Daular Musulunci ta (IS) sun harbo wani jirgin yaki mallakar kasashen kawance da Amurka ke jagoranta a arewacin kasar Siriya, inda suka…

Mayakan kungiyar kafa Daular Musulunci ta (IS) sun harbo wani jirgin yaki mallakar kasashen kawance da Amurka ke jagoranta a arewacin kasar Siriya, inda suka tasa keyar matukinsa, dan kasar Jordan.
Wata kungiyar kare hakkin Bil-adama ta Siriya da ke da cibiyarta a Landan, ta ce an harbo jirgin ne a kusa da birnin Rakka da ke karkashin ikon kungiyar IS. Babu bayanai kan yanayin da jirgin ke ciki. kasar Jordan na cikin kasashen Larabawa da ke yaki da kungiyar IS.
kungiyar ta wallafa hotunan direban jirgin, wanda aka bayyana sunansa da Laftanar Youssef al-Kasasbeh. Kuma wannan ne karon farko da IS ta harbo jirgi mallakar kasashen kawance da Amurka ke jagoranta tun lokacin fara kai wa kungiyar farmaki a watan Satumban da ya gabata. kasar Jordan ta tabbatar da kama jirgin nata a wata sanarwa daga kamfanin dillancin labaran kasar.
Masana dai sun ce ba za a iya fahimtar abin da ya faru kafin kamun jirgin ba, wata kila ko ya samu matsalar na’ura, ko kuma kakkabo shi mayakan IS din suka yi. A baya dai mayakan kungiyar sun sha harbo jiragen kasashen Siriya da na Iraki. Kuma a yanzu haka akwai yankuna da dama da ke karkashin ikonsu ciki har da sansanin sojojin saman kasar Siriya.