✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mazabar Bichi ta saya wa dan majalisa fom din neman tazarce

Al’ummar mazabar Bichi sun yi wa Honarabul Abubakar Kabir karo-karon Naira miliyan 28.

Al’ummar mazabar Bichi sun yi karo-karon Naira miliyan 28 domin saya wa Honarabul Abubakar Kabir Bichi fom din neman takarar dan Majalisar Wakilai na jam’iyyar APC.

Wannan dai na zuwa ne a matsayin rama wa Kura kyakkyawar aniyarta da kuma yaba wa kwazon Honarabul Bichi da al’ummar mazabarsa suka yi, la’akari da yadda suka sharbi romon dimokuradiyya da kuma sauran ababe na ci gaba da ya kawo musu, musamman yadda ya wadata hanyoyin neman ilimi ga duk ’yan asalin Karamar Hukumar ta Bichi.

Kungiyar Dalibai ta Hon. Abubakar Kabir Students Association (HAKASA) ce ta gudanar da bikin karo-karon kudin ranar Lahadi a Makarantar Firamaren Haggagawa da ke Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, daga cikin wadanda suka bayar da gudunmuwa mai tsoka a karo-karon kudin da aka siya masa fom din neman takarar sun hada da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Injiniya Rabiu Suleiman Bichi da Sanata Barau Jibrin, wakilin Shiyar Kano ta Tsakiya a Majalisa Dattawa da Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Farfesa Yusuf Muhammad Sabo, Honarabul Lawan Shehu Bichi, daya daga cikin wakilai na Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Sauran sun hada da Shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Kano ta Arewa, Alh. Sani Mukaddas, Ma’ajiyar jam’iyyar APC ta Kano, Haj. Yardada Maikano, Malamai 106 da ya dauka aikin koyar da darussan kimiyya a Makarantun Sakandire daban-daban na Karamar Hukumar Bichi tun daga shekarar 2020 zuwa yanzu da kuma daruruwan masu sharar titi da ya dauka aiki da sauransu.

A cewar wasu daidaikun mutane da suka gabatar da jawabai yayin taron, sun ce wannan gudunmuwa tilas ce duba da yadda dan majalisar ya inganta rayuwar al’umma a Bichi.

Sun ce daga shekarar 2019 zuwa yau, Honarabul Abubakar Kabir ya dauki nauyin karatun fiye da dalibai 5000 a Karamar Hukumar ta Bichi domin yin karatu a jami’o’i da manyan makarantu a ciki da wajen Jihar Kano.

Haka kuma, sun ce dan majalisar ya dauki nauyin fiye da mutum 500 ’yan asalin karamar hukumar domin yin karatu a Makarantun Sakandire na Kimiyya da Fasaha da ke Kano.

Ana iya tuna cewa, a watan Yulin 2021 da ya gabata ne Kwalejin Tarayya ta Bichi ta bai wa Honarabul Abubakar lambar yabo ta Fellow of Education a matsayin karamci na daukar nauyin karatun al’umma da ya saba yi.

A bayan nan ne dai jam’iyyar APC ta kayyade Naira miliyan 10 a matsayin kudin sayen fom da kuma na bayyana manufar tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai.