✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Monaco ta yi wa Arsenal sakiyar da ba ruwa

A shekaranjiya Laraba ne kulob din Arsenal da ke Ingila ya sha kashi a wajen na Monaco da ke Faransa da ci 3-1 a gasar…

A shekaranjiya Laraba ne kulob din Arsenal da ke Ingila ya sha kashi a wajen na Monaco da ke Faransa da ci 3-1 a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) da aka yi a filin wasa na Arsenal da ke Ingila.

Wasan ya ba magoya bayan Arsenal mamaki, don wasa ne da aka dauka kulob din Arsenal ne zai lallasa na Monaco sai aka samu akasin haka.
Idan za a tuna, kocin Arsenal na yanzu Arsene Wenger ya taba zama kocin Monaco a shekarar 1988 kafin ya koma na Arsenal din.
Yanzu Arsenal za ta bi Monaco gida ne don yin wasa zagaye na biyu a ranar 19 ga watan gobe idan Allah ya kaimu don tantance kungiyar da za ta haye matakin kwata-fainal.
A daya wasan kuma, kungiyar kwallon kafa ta Bayern Leberkusen ce ta lallasa ta Atletico Madrid da ci daya mai ban haushi. Rabon da Leberkusen ta kai wasan karshe tun a shekarar 2002 a wasan karshen da ta yi da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.