✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulma ta raba wa marayu da zawarawa Kirista kayan Kirsimeti a Kaduna

A wannan hali da matsin rayuwa, wata Musulma ta raba kudi da tufafi ga marayu da zawarawa da ’yan gudun hijira Kiristoci domin su yi…

A wannan hali na matsin rayuwa  da tsadar kayan masarufi, wata Musulma, Ramatu Tijjani ta raba kudi da tufafi ga marayu da zawarawa da ’yan gudun hijira Kiristoci a Kaduna domin su yi bukukuwan Kirsimetin bana.

Ramatu Tijjani wadda ke harkokin hada kan mabiya addinai, ta ce a watan Ramadan, Fasto Yohanna Buru, Babban Limamin Cocin, yakan raba wa talakawa Musulumi buhunan abinci da suke amfani da shi a cikin watan mai alfarma.

Ta ce manufar rabon nata ta ita ce tallafa wa matan da mazansu suka mutu da ’yan gudun hijira da gidajen marayu sama da 200 a lokacin Kirsimeti da zummar wanzar da zaman lafiya, kaunar juna da juriya a tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Hajiya Ramatu ta bayyana sha’awarta ta sanva farin ciki da jin dadi ga zawarawa, tare da ba su damar gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin farin ciki kamar kowane Kirista.

A yayin rabon tallafin a Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke unguwar Gbagwi Villa Kaduna, ta ce, “Kirsimeti ya ba wa Musulmi babbar dama su nuna wa makwabtansu Kirista cewa Musulunci addini ne na zaman lafiya, soyayya da kuma juriya.

“Ina so in ga zawarara, marayu da tsofaffi a lokacin Kirsimeti suna murmushi da farin ciki kamar kowane iyali na Kirista a lokacin bukukuwa irin wannan.”

Ta kara da cewa a lokacin Sallah , Kiristoci da yawa sukan aika mata da kyaututtuka domin ta raba wa Musulmi marasa galihu.

Don haka ta jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin mabiya addinai da kuma taimaka wa matan da mazansu suka mutu da marayu, ba are da la’akari da bambancin kabila, addini ko yanki ko harshe ba.

 Ramatu Tijjani ta jaddada kudirinta na sanya farin ciki ta hanyar raba kayan abinci da sauransu a coci-coci a Kaduna da wasu jihohin, domin ba da gudummawar farin ciki ga zawarawa a lokacin bukukuwan.