✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulmin Arewa ba ya da aiki sai zagin malamansa

Kwarai na san me karatu zai yi mamaki.

Ina wannan rubutu cike da mamaki da bakin ciki mara misaltuwa wanda har ya yi sanadiyar kasa yin cikakken barci gare ni.

Hakan ya faru ne saboda nazari da kirdadon yadda Musulmin Arewa suke yi wa kansu da kansu illa ta wajen rashin nuna sanin ya kamata, tare da tozarta asalinsu na tsarin koyar da tarbiyyar addinin Musulunci.

Wannan shi ya janyo mana duk wani hali da muke ciki, domin malaman sun koma wani tsari daban wanda ba shi ne hanyoyin da’awa a addinin Musulunci ba.

Su kuma mabiya sun bi wata hanyar daban kamar yadda Bahaushe yake cewa “An yi hannun riga.”

Mai karatu ka ga sai abin da aka gani ke nan!

Akwai wasu tambayoyi da ya kamata a yi tadabburi a kansu kamar haka; wai shin malamanmu na addini suna bin hanyoyin da Annabi (SAW) da sahabbai suka koyar da mu da’awa kuwa?

Kuma suna kokari su koya wa mabiyansu wadannan hanyoyin kuwa?

Kuma suna kare addinin Musulunci ne ko suna kare kungiyoyinsu?

Wadannan tambayoyi da na kawo a sama, ya kamata duk wani Musulmin Arewa ya amsa wa kansa domin kubuta daga tarkon barin kare addini zuwa kare kungiyoyi.

Abu mafi muni shi ne Musulmi ya bar kare addininsa, ya koma kare akidarsa da malamansa.

Dadin dadawa ya koma daina ganin duk wani malami wanda ba daga bangaren akidarsa ya fito ba a matsayin malamin addini.

Addinin Musulunci ya zo mana da koyarwa ta yadda ake tausasa lafazi ga na sama da masu shekaru, ya koyar da mu girmama duk wanda ya fi ka a ilimance.

Sannan ya koyar da mu yadda za mu yi gyara ga duk wanda ya yi kuskure ta hanyar yi masa zance mai dadi da tausasawa.

Amma ko ina muka bar wannan tsari?

Na san mai karatu zai taya ni laluben wannan amsa. Hadin kan al’umma su zama daya, kullum shi ne abin da muke kiran dukkan Musulmin duniya a kai.

Wannan shi ne abin da ya kamata malamanmu su koma koyarwa a majalisun karatuttukansu, ba su mai da hankali a kan koyar da su karatun raddi ba.

Karatun raddi kuwa kawai ina daukarsa a kan karatun neman suna da shahara domin kawai malami ya samu wani tumunin duniya sai dai muna addua Allah Ya tsare imaninmu!

Wallahi tallahi, malaman nan namu akwai sauran aiki a gabanku domin kuwa akwai tarin Musulmi a Arewa, kai har ma a cikin dalibanku wadanda ba su iya Sallah ba balle a zo maganar ilimin zamantakewa.

Kwarai na san me karatu zai yi mamaki. Wannan ya samo asali ne ta dalilin barin tsarin koyarwa da malaman suka yi suka koma ga tsarin koyarwar karatun musu ko jayayya da zagin juna.

Babbar matsalar ita ce, kowane malami idan ka tsaya ka saurare shi, sai ka ji so yake ya nuna wa dalibansa shi ne ya fi kowa ganewa duk sauran ba su gane ba.

To don Allah mai karatu akwai wani mutum daya da zai ce ya fi kowa ilimi, ko ganewa?

Kuma irin wannan bakin hali ana samunsa a kowane bangaren malaman.

A ganina kamata ya yi mu rika girmama sabanin fahimta idan har wannan abin bai saba da mizanin shari’a ba.

Amma duk da wannan bakin halin da ya yi yawa a cikin malamai, akwai da yawa a cikinsu wadanda suke kamantawa sosai daga kowane bangare kuma bamu da ta cewa sai dai mu ce Allah Ya saka musu da alheri!

Muna kira da su taimaka wajen jan hankalin ’yan uwansu malamai idan sun kauce hanya. Domin hakan zai taimaka kwarai da gaske.

Ina amfani da wannan dama in ja hankali ga mabiya su natsu, su yi gyara halinsu, domin kada malamai su kai su ga hallaka ta wajen sa su yin zagi ko izgilanci ga ’yan uwansu malamai.

Idan har dan uwa mai karatu zai bi wannan tsarin, insha Allah zai ga wani sabon canji na gaggawa a cikin tsarin neman iliminsa da rayuwarsa gaba daya.

A karshe ina rufewa da cewa; Ya Allah Ka raba mu da neman ilimin addinin Musulunci don samun wani abin duniya, ko zama malami don yin karatun jayayya ko yada abubuwa masu rikitarwa.

Ya Allah! Ka raba mu da karatun raddi. Ya Allah! Ka sa mu cikin wadanda za su zama sanadiyyar hadin kan Musulmi.

Ya Allah! Ka sa mu rika girmama duk wani dan Adam ko da ba Musulmi ba ne.

Ya Allah Ka saka wa malamanmu da alheri da suka tarbiyyantar da mu a kan tarbiyyar hadin kan al’umma ta hanyar girmama duk wani mai amsa kalmar “La’ilaha illallahu.”

Daga Khalid Sunusi Kani, Za a iya samunsa a [email protected] ko 07030631259