✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nadi APC ta yi a Zaben Kananan Hukumomin Gombe —PDP

Wakilan PDP sun kari zamansu a rumfunan zabe ba su ga turawan zabe ko kayan zabe ba

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi fatali da abun da ta kira dauki-dora da jam’iyyar APC ta yi da sunan zaben kananan hukumomi a Jihar Gombe.

Shugaban PDP a Jihar, Abnon Kalayi Kwaskebe, ya yi Allah wadai da zaben a lokacin taron ’yan jarida a Sakatariyar jam’iyyar ta jihar.

Kwaskebe, ya yi watsi da sakamakon zaben ba domin a cewarsa Hukumar Zabe ta Jihar (GOSIEC) da jam’iyyar APC ne suka zauna suka shirya almundahana da sunan zaben bayan sun gaya wa duniya cewa za su gudanar da sahihin zabe.

A cewarsa, ko a lokacin da Shugaban GOSIEC ta sanar da sakamakon zaben, bai fadi yawan kuri’un da aka jefa wa kowane dan takara ba balantana a san yawan kuri’un da suka lalace.

Ya ce akwai runfunan zabe 2,218 a Jihar Gombe kuma duk sun tura wakilansu, amma wakilan suka gama zamansu a rumfunan zabe ba tare da sun ga malaman zabe ko kayan zaben ba.

Shugaban na PDP ya ci gaba da cewa ba su yi mamakin faruwar hakan ba domin APC ta riga ta fada a lokacin kaddamar da yakin neman zabenta cewa ba za su yi zabe ba domin ba wata jam’iyyar da ke takara bayanta.