✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Nahiyar Afirka na canzawa cikin hanzari’

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce nahiyar Afirka na samun ci gaba kuma ta canzawa cikin hanzari. Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabinsa…

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce nahiyar Afirka na samun ci gaba kuma ta canzawa cikin hanzari.
Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ranar karshe a taro kan nahiyar wanda aka kammala shekaranjiya Laraba a birnin Washington.
Taron wanda shugabannin kasashen nahiyar fiye da 40 suka halarta. Wanda kuma ya tattauna kan yadda za a samar da tsaro da magance matsalar cin-hanci da rashawa, bangarori biyu da gwamnatin Amurkar ta ce suna kawo cikas ga ci gaban nahiyar. A lokacin taron na kwana uku, wani kamfanin Amurka ya yi alkawarin zuba jari da kudin da suka kai Dala biliyan 14.
Kodayake  Sakataren Harkokin Wajen kasar John Kerry ya shaida wa shirin turanci na HardTalk na kafar yada labarai ta BBC cewa, za a yi amfani da kudin ne don yakar ayyukan ta’addanci da ke karuwa a nahiyar. Ya ce: “Za a ga raguwar ayyukan ’yan kungiyar Boko Haram da ’yan al-Shabab saboda idan aka samu masu zuba jari, za a samu wadatuwar ayyuka wanda zai hana jama’a shiga ayyukan ta’addanci. ”
A lokacin jawabin da ya gabatar ranar Laraba, Mista Obama ya ce nahiyar Afirka nahiya ce mai tasiri kuma tana canzawa cikin sauri duk da irin kalubalen da take fuskanta ciki har da barazana daga annobar cutar Ebola.
A bangaren guda kuma, Uwargidan Shugaba Obama Michelle ta shirya wani taro kan harkokin ilimi da lafiya ga matan shugaban da suka halarci taron.