✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

… Nakasassu a Jihar Filato sun ce ba su ba PDP

Ko’odinetan kungiyar Nakasassu ta Najeriya reshen Jihar Filato Mista Bulus Shanding ya umarci ’ya’yan kungiyar kada su zabi dan takarar kowane mukami a karkashin Jam’iyyar…

Ko’odinetan kungiyar Nakasassu ta Najeriya reshen Jihar Filato Mista Bulus Shanding ya umarci ’ya’yan kungiyar kada su zabi dan takarar kowane mukami a karkashin Jam’iyyar PDP a kasar nan.

Mista Shanding ya ce ’ya’yan kungiyar sun dandana kudarsu a karkashin mulkin PDP a matakin tarayya da jiha. “Mu nakasassu muna da yawa a kasar nan, mu miliyan 24 amma mutane suna ajiye mu a gefe. Mu ma fa ’yan Najeriya ne muna son a rika damawa da mu a harkokin jama’a don haka muna son wannan canji.”
Bayan doguwar tattaunawa da wasu ’ya’yan kungiyar nakasassun a Jos a ranar Litinin, sai ya bukaci nakasassu a jihar su zabi dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari da kuma dan takarar Gwamnan Jihar na APC Mista Simon Lalong a zaben 28 ga Maris da 11 ga Afrilu.
Mista Shanding ya ce nakasassu sun kafa wata kungiyar siyasa mai suna “Disability Support Group” domin mara wa ’yan takarar APC a jihar da tarayya.
Ganawar ya samu halartar Daraktan Jawo Ra’ayin Nakasassu na Jam’iyyar APC na kasa Samuel
Mista Shanding ya ce “da tsintsiyoyinmu za mu shawo kan nakasarmu mu share kama-karya da danniya da watsi da mu da kuma tauye mana ’yancinmu na dan Adam.”
A nasa bangare Mista Ankeli, ya ce “APC ta tsara mana makoma, kuma hakan ya nuna sun shirya gwamnati ta kowa da kowa don haka muna nan ne domin kiran jama’armu don cimma nasarar APC. Don haka muna kira ga ’ya’yanmu su zabi dukkan ’yan takarar APC domin muna da tabbacin za su tafi tare da mu a harkokinsu.”
Shugabannin sun bukaci shugabannin APC su tabbatar shelar canji da ke kankama a tsakanin nakasassu ta haifar da sakamako mai kyau ta hanyar tsoma su a cikin harkokinsu.