✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nakiyar Boko Haram Ta Hallaka Manoma A Borno

Wata nakiya da mayakan Boko Haram suka binne ta hallaka manoma bakwai a cikin wata motar haya a Jihar Borno.

Wata nakiya da mayakan Boko Haram suka binne a kan titin Pulka/Firgi da ke Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno, ta hallaka manoma bakwai a cikin wata motar haya.

A safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, 2024, abin motar da ke dauke da wadanda abin ya shafa ta bi ta kan nakiyar da ’yan ta’addan suka dasa.

Majiyoyin sun ce an tabbatar da mutuwar fasinjoji bakwai wadanda manoma ne da direban motar a yayin da  wasu bakwai suka samu munanan raunuka.

’Yan ta’addan sun dauki wannan salon ne ganin cewar dakarun sojin Najeriya sun dukafa ka’in da na’in don ganin bayansu ko ta halin kaka.

Majiyoyin tsaro na nuna cewar, nakiyoyin da aka dasa a baya-bayan nan sun yi sanadin salwantar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba — galibinsu yara mata a jihar Borno.

“Wadannan bama-bamai, da akasarinsu na cikin gida ne, su ne ’yan ta’addan suka rika amfani da su tun lokacin da suka fara tada kayar baya a yankin nan na Arewa maso Gabas da suka kai ga halaka dubban jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba,” in ji majiyar.