✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NBC ta ci manyan gidajen talabijin tara kan #EndSARS

Hukumar Dake Kula da Kafafen Watsa Labarai ta Kasa (NBC) ta ci wasu gidajen talabijin tarar Naira miliyan tara saboda rahotannin da suke yadawa kan…

Hukumar Dake Kula da Kafafen Watsa Labarai ta Kasa (NBC) ta ci wasu gidajen talabijin tarar Naira miliyan tara saboda rahotannin da suke yadawa kan zanga-zangar #EndSARS.

Tashoshin da tarar ta shafa sun hada da tashar talebijin ta Channels da AIT da tashar Arise TV.

NBC ta ci kowanne daga cikin gidadjen talabijin din tarar Naira miliyan uku saboda nuna rashin kwarewa wurin fitar da rohotannin abubuwan da suka faru a zanga-zangar ta #EndSARS.

Mukaddashin Babban  Daraktan hukumar, Farfesa Armstrong Idachaba ne ya fitar da sanarwar ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin.

Sauran karin bayani zai zo daga baya.