✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDE ta bai wa matasa 1000 horo kan sana’ar hannu a Jigawa

A karshen makon jiya ne Hukumar NDE ta bai wa matasa dubu daya horo, a kan yadda zasu rika yin man shafawa da sabulun wanki…

A karshen makon jiya ne Hukumar NDE ta bai wa matasa dubu daya horo, a kan yadda zasu rika yin man shafawa da sabulun wanki da wanka da turaren jiki da na tufafi ga maza da mata.

Alhaji Sani Lawan daya saga cikin manyan shugabannin hukumar ta NDE a Jihar Jigawa, ya ce an zakulo masu bada horon ne daga daukacin kananan hukumomin jahar 27.

Ya ce makasudin bai wa matasa wannan horon shine dan samar da ayyukan yi a tsakanin matasan, domin su zama masu dogaro da kansu.

Yana mai cewa maza kuma za a horas da su kafinta da gyaran waya da gyaran babura tare da koyar da su ayyukan walda. Kuma za a rika ba su alawus na naira dubu biyu. Yayin da matan zasu yi mako biyu wajan samun horon, inda su kuma mazan zasu yi wata uku suna samun horon.

Daga nan ya hori matasan du su zama masu neman ilimi domin sai da ilimi ne ake samun cigaban rayuwa, haka zalika ya hori matasan da aka baiwa horon su yi amfani da irin abin da suka koya a matsayin sana’ar da zasu iya rike kansu.

Ya ce da zarar matasan sun kammala samun horon, Hukumar NDE zata basu kayayyakin sana’ar kuma zata ba su jari. Haka zalika ya ce zasu sanya idanu akansu domin ganin sun ci gaba da yin sana’ar da aka gwada masu.

Ya kara da cewar duk wanda suka samu ya sayar da kayan sana’ar da aka ba shi, to ya kuka da kansa, domin hukumar ba za ta amince da hakan ba, a cewarsa.