✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neja Tornadoes ta sake haurawa gasar rukunin Firimiya ta kasa

Kulob din Neja Tornadoes da ke Minna ya samu nasarar hayewa gasar rukuni-rukuni na Najeriya da ake wa lakabi da Nigeria Professional Football League (NPFL)…

Kulob din Neja Tornadoes da ke Minna ya samu nasarar hayewa gasar rukuni-rukuni na Najeriya da ake wa lakabi da Nigeria Professional Football League (NPFL) bayan ya zama zakara a rukunin da ya fafata..&nbsp Kulob din ya samu nasarar haka ne bayan ya lallasa kulob din Mighty Jets da ke Jos a ranar Asabar da ta gabata da ci 2-0.&nbsp Wasan ya gudana ne a filin wasa na Bako Kwantagora da ke Minna.&nbsp Kulob din ya fafata ne a rukunin da suka hada da kungiyoyi bakwai ciki har da na Gombe United da ABS da kuma na Maighty Jet da ke Jos.
A shekarar 2012 ne kulob din ya koma gasar rukunin ’yan dagaji (amateur) bayan kulob din Rising Stars ya lallasa shi da ci daya mai ban haushi a wasan karshe.&nbsp &nbsp Sai ga shi a wannan karo kulob din ya sake komawa gasar rukunin firimiya bayan ya samu nasara a kan Mighty Jets.
’Yan kwallon Tornadoes biyu Yakubu Alfa da Samson Adeyemi ne suka jefa kwallaye biyu a ragar Mighty Jets da hakan ya ba kulob din damar komawa gasar rukunin firimiya ta kasa.