✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Otal mai hawa 4 ya danne mutum 20 a Abuja

Ana fargabar ya danne mutum 20 a cikinsa

Wani gini mai hawa hudu da ake aikin ginawa, mallakin wani otal a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, ya rushe kuma ana fargabar ya danne kusan mutum 20 da ke cikinsa.

Otal din, mai suna Summit Villa dai na yankin Dape ne a unguwar Life Camp, ya rushe ne da yammacin Litinin.

A cewar wani ganau a inda lamarin ya faru, otal din wanda kuma yake da ginin karkashin kasa, ana fargabar ya danne sama da mutum 20.

Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, wakilinmu ya ce an sami nasarar ceto tara daga cikin mutanen da ginin ya danne.

Tuni dai jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), suka isa wurin inda suke dukufa aikin ceto mutanen da ke ciki.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, ba a samu rahoton samun asarar rai ba.