✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PIB: Majalisa ta amince da dokar man fetur

Bayan shekaru ana kai-komo, Majalisar Tarayya ta amince da dokar mai ta PIB.

Zauren Majalisar Tarayya ya amince da dokar Man Fetur ta PIB bayan shafe shekaru ana kai-komo a kan sarkakiyar kudurin dokar.

Majalisar ta amince da dokar ce bayan Shugaban Kwamitinta na wucin-gadi kan  PIB, Mohammed Monguno, ya gabatar da rahoto kan kudurin dokar, wanda ya samu amincewar mutum 319 daga cikin ’yan Majalisar.

Bayan amincewa da dokar, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce, “Karyar ‘kwankwaman’ PIB ta kare, yanzu mun amince da ita.”

Ahmad Lawan ya jinjina wa kwamitin da daukacin Majalisar kan aiwatar da dokar.

Shi ma a jawabinsa, Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yaba wa Majalisar Tarayya da “Suka zama abin alfaharin ’yan Najeriya.”

A jawabinsa, Monguno ya ce amincewa da dokar babbar nasara ce a aikin kafa dokoki da Majalisar ta yi, zai kuma taimaka wajen tabbatar da yin komai a fili tare da kuma bunkasa harkokin albarkatun mai.

Tun da farko sai da Kwamitin Man Fetur na Majalisar ya gabatar da rahotonsa kan kudurin dokar wanda zauran Majalisar ya bi shi daki-daki sannan ya amince da shi.