✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Plateau United ta ci gaba da jagorantar Gasar Firimiya

Bayan da kungiyar kwallon kafa ta Plateau United ta doke Jigawa Golden Stars da ci 2-1 a wasan mako na 22 na gasar Firimiya ta…

Bayan da kungiyar kwallon kafa ta Plateau United ta doke Jigawa Golden Stars da ci 2-1 a wasan mako na 22 na gasar Firimiya ta Kasa a ranar Lahadi, kungiyar ta ci gaba da zama ta daya a teburin gasar.

Sashin Hausa na BBC ya ce, tun kafin a je hutun rabin lokaci Plateau ta ci kwallo ta hannun Salefu Oche Ochowechi, sannan Tosin Omoyele ya ci ta biyu saura minti takwas a je hutun.

Daf da za a tashi daga wasan ne Jigawa ta jefa kwallo daya ta hannun Saleh Ibrahim. Da wannan sakamakon Plateau ta sake ci gaba da darewa saman teburin gasar da maki 40 da tazarar maki daya tsakaninta da Ribers United mai maki 39, sai Lobi Stars maki 39.

Jigawa Golden Stars kuwa tana ta 19 da maki 23 da tazarar maki uku tsakaninta da Adamawa United ta karshen teburi wato ta 20.