✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rage kudin man fetur: Wasu sun yaba wasu sun koka

A yayin da gwamnatin tarayya ta bayyana rage kudin man fetur daga naira 97 zuwa 87 ra’ayin al’ummar Jihar Legas ya rabu gida biyu, inda…

A yayin da gwamnatin tarayya ta bayyana rage kudin man fetur daga naira 97 zuwa 87 ra’ayin al’ummar Jihar Legas ya rabu gida biyu, inda wasu suka yaba da matakin wasu kuwa suka yi Allah-wadai da rage farashin.

Malam Sani Murtala ya shaida wa Aminiya cewa gwamnati ta rage farashin ne don cimma burin siyasa.
“Ni ina ganin gwamnati ta rage farashin ne don ta ga zabe ya kawo jiki. Saboda haka tana so ta yi amfani da rage farashin ne don cimma burinta na siyasa. Ba sa yin abu don talakawa, ai da don talakawa suke yi da tuntuni sun rage farashin, amma ba su yi haka ba sai yanzu da zabe ya zo. Mu dai muna kira a gare su da su ji tsoron Allah su rika tausaya wa talakawa don man fetur ya zama tamkar ruwa zinare farashinsa yana shafar talaka,” inji shi.
Shi ma Malam Musa Haladu cewa ya yi “Ba ma maraba da rage farashin man da suka yi. Da can ba su rage ba sai yanzu da suka ga za su fadi zabe shi ya sa suka rage. Ko su rage ko kar su rage ba za mu zabe su ba. Gara ma su bar shi a yadda yake. Tunda ko lokacin da ma muna sayansa fiye da naira 97 kuma ba mu mutu ba.”
Shi kuwa Mista Olorufunwa ya yaba da matakin da gwamnati ta dauka inda ya ce: “Babu shakka gwamnati ta yi abin da ya dace da ta rage farashin mai a yanzu. Don talakawa sun dade suna cikin matsi saboda tsadar da man fetur ya yi. Saboda haka dole mu yaba mata mu kuma jinjina mata ba tare da nuna bambancin siyasa ba.”
Malam Yahuza Salisu shi kuwa kira ya yi ga gwamnati ta kara rage farashin don saukakawa talakawa. Ya ce: “Rage farashin da gwamnati ta yi ya yi kyau amma akwai sauran rina a kaba saboda haka muna kira ga gwamnatin tarayya ta kara rage kudin man don zai sa kayayyakin masarufi su sauko talakawa ya saya da sauki ba tare da wata matsala ba,” inji shi.