✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rigakafin barkewar Tashin Hankali Bayan Zaben Bana

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina (08165270879), ya yi nazari game da al’amuran siyasar Najeriya, sannan ya zayyana wasu shawarwari da yake ganin idan aka…

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina (08165270879), ya yi nazari game da al’amuran siyasar Najeriya, sannan ya zayyana wasu shawarwari da yake ganin idan aka bi za su yi maganin barkewar rikici a Najeriya, bayan an kammala zabubbukan bana. Ga abin da yake cewa:

Da ba don dan Najeriya mutum ne mai saurin mantuwa ba, to da za a dauki lokaci mai tsawo bai a manta da mummunan rikicin da ya biyo bayan zaben 2011 ba, wanda ya lakume rayukan mutanen da ba su ci ba, ba su sha ba. A kiyasin wani bincike da kungiyar Kare ’Yancin dan Adam ta yi, ta ce an kashe mutane 800.
A wannan kididdiga: “A Giyade a Bauchi, masu tarzoma sun far wa ’yan bautar kasa da suka yi aikin kidaya kuri’u a wani ofishin ’yan sanda, suka kashe ’yan sanda da ke kan aiki tare da kona ofishin ga baki daya, suka kuma yi wa ’yan mata guda biyu masu bautar kasa fyade tare da yi masu gunduwa-gunduwa” (binciken Cibiyar Raya Dimokuradiyya ta Friedrich Ebert Stiftung).
To ba a nan abin ya tsaya ba, domin hatta sarakunanmu da sauran shugabanni na Arewacin Najeriya sun dandana kudarsu. Misali, an far wa gidan Mai alfarma sarkin Musulmi, kazalika an kai hari gidajenn sarakunan Kano, Zazzau da na Galadiman Kano da sauran jiga-jigan Arewacin Najeriya. Matasan ma har motar Janar Buhari suka kai wa hari. Wani abin tunawa shi ne, yadda rikicin ya rikide ya koma na addini, inda a garin Zonkuwa an kashe Musulmi da yawa da sunan ramuwar gayya.
Shin yanzu wane mataki aka dauka don hana sake afkuwar abin da ya faru a 2011, don kar ya sake wakana a bana? Domin idan muka kalli salon siyasar yanzu, kusan ba ta canza daga ta 2011 ba. ’Yan takarar manya sun fito daga addinai daban-daban. Buhari Musulmi daga APC, Jonathan Kirista daga PDP. Shakka babu Buhari ya fi Jonathan yawan magoya baya a Arewa, yayin da Jonathan ke tinkahon yawan magoya baya a Kudu maso kudu da Kudu maso gabas.
Tabbas wannan abin dubawa ne. Kazalika, tun kafin zaben, tuni kowane bangare ke barazanar cewa idan bai ci zabe ba zai tada hankali. Misali, shugaban kungiyar Tsagerun Matasan Neja-Delta Asari Dokubo, ba irin kalaman batanci da bai fadi ba a kan al’ummar Hausa/Fulani Musulmi. Ya sha fada cewa ba za su taba yarda Hausa da Fulani Musulmi ya kara mulkin Najeriya ba. Ya ma taba barazanar kashe Farfesa Ango Abdullahi.
Baya ga Asari akwai sauran mutanen yankin Neja-Delta kamar Chief Edwin Clark, wanda ya sha nanata cewa dole Jonathan ya ci zabe, ko kuwa babu sunan wata kasa Najeriya bayan zaben 2015.
Mu ma ta bangaren Arewa, duk da muna taka-tsan-tsan amma wadansu kan maida martani mai zafi, mutane kamar su Bala Ibin Na’Allah da sauran su. Baya ga kalamai masu zafi da ke fitowa daga sassa daban-daban na kasar nan, akwai batutuwa da dama da suka faru cikin wannan zangon masu matukar hadari da muni; wadanda ba mu san su a 2011 ba. Misali, batun yi wa ’yan Arewa mazauna Kudu rijista. Batun ya jawo martani mai zafi daga ’yan Arewa, inda har wata kungiya, a karkashin jagorancin Barista Bulama ta dauki nauyin wani kudirin doka da zai tilasta yi wa ’yan Kudu rijista a Arewa.
Babban batu mai matukar barazana, wanda ya kara raba kawunan kasar shi ne, rikicin Boko Haram, inda ’yan Arewa ke hasashen makarkashiya ce ake mata saboda haka zaben bana.
Lalle wadannan su ne abubuwa masu hadari, wadanda ake ganin sun sanya kasar cikin tsaka-mai wuya.
Me ke mafita? Ya za a hana barkewar rikici bayan an sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa na bana? A nan dole ne mu koma baya mu duba rahotannin da kwamitocin da aka kafa bayan rikicin zaben 2011, mu ga wanne aka aiwatar, wanne ne kuma ba a aiwatar ba. daya daga cikin fitattun kwamitocin shi ne na Sheikh Ahmed Lemu, wanda ya ba da rahotansa a ranar 10 ga watan Oktoba, 2011. daya daga cikin abubuwan da kwamitin ya gano shi ne gwamnatocin baya ba su hukunta masu hannu a ta da tarzoma.
A cewarsa: “Wannan ne ya jawo kowa ke abin da ya ga dama domin ba abin da zai faru.” Abin tambaya a nan gaba shi ne, mutum nawa aka hukunta bayan kammala rikicin bayan zaben 2011? Ni dai a iya sani na, ban ji labarin mutum daya da aka gurfanar da shi, aka hukunta shi bisa aikata laifin zabe ba. Wadanda aka kashe, sun mutu, sai dai a lahira a bi masu hakkinsu amma ba dai a Najeriya ba. Sauran abubuwan da kwamitin ya gano masu alaka da ingiza matasan tafka danyen aikin da suka tafka sun hada da talauci, bangar siyasa, mulkin-a-mutu-ko-ai-rai da sauransu. Da Alama babu wani matakin a zo a gani da gwamnatoci suka dauka don dakile wadannan matsaloli. Kada mu manta da kalmar karshe ta Lemu, cewa har in aka gaza daukar mataki, to kasar za ta iya fuskantar bore shigen abin da ya faru a wasu kasashen Larabawa.
To mu dai muna ji, muna gani, muna kuma saurare amma dai Hausawa na cewa kowa ya ki ji, to ba ya ki gani ba. Idan ’yan siyasa basu kare bakunansu ba da watsar da siyasar-a-mutu-ko-ai-rai, to kuwa ba a gama zubar da jinin mutane da sunan dimokuradiyya a Najeriya ba. Sai dai matasa, wadanda da su ake amfani wajen aikata rikice-rikice su sani, babu wata riba da suke ciki. Za a yi amfani da su, sannan a watsar da su daga karshe.