✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin APC a Bauchi ya dauki sabon salo

Shugabannin Jamiyyar APC na kananan hukumomin dake Jihar Bauchi sun bayyana cewa sun dakatar da shugaban Jam’iyyar na Jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmed Nana. Shugaban…

Shugabannin Jamiyyar APC na kananan hukumomin dake Jihar Bauchi sun bayyana cewa sun dakatar da shugaban Jam’iyyar na Jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmed Nana. Shugaban Jamiyyar APC na Karamar Hukumar Bauchi, Alhaji Rabiu Shehu Danbaba ne ya karanta jawabin, bayan taron da shugabannin suka yi ga manema labarai a wannan makon.

Ya ce, “Yanzu haka mun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi Hon. Uba Ahmed Nana, kuma daga dakatar da shi mun nada Shugaban APC na karamar Hukumar Shira, Alhaji Aminu Shehu Na-Borno a matsayin wanda zai rike shugabancin wannan Jam’iyya, sannan kuma mun kafa kwamitin bincike wanda wannan kwamiti su ne za su binciki Alhaji Uba Ahmed Nana dukkan abubuwan da muke zargi akansa wadanda suna nan da yawa, idan sun same shi da laifi shike nan,  idan kuwa ba su same shi da laifi ba, sai mu dawo da shi kan matsayinsa”

Rabi’u ya ce suna zarginsa da kasa tafiyar da jam’iyya yadda ya kamata, kuma shi kadai yake tafiyar da jam’iyyar ba tare da Sakatare da  Ma’aji ba, kuma wannan jam’iyya ko asusun banki ba ta da shi.

Ya ce wannan mataki da suka dauka zai kawo martaba da karfi da ci gaba ga jam’iyyar domin zai magance yawan korafe-korafe da zarge-zarge da mutane ke yi a ko’ina cikin jiha cewa ba ta iya aiwatar da komai na jagoranci a jamiyyar, wanda inda da jagoranci mai kyau haka ba za ta faru ba.

Rabiu ya ce an kafa kwamiti mai wakilai biyar karkashin jagorancin  mataimakin mai binciken kudi na jiha, Alhaji Auwal Sallau don gudanar da bincike kan tsohon shugaban. Shugabannin sun kuma jaddada goyon baya da biyayyansu wa shugabancin jam’iyyar na kasa da kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar.

Da yake maida martani ga manema labarai ta wayar tarho kan al’amarin, Shugaban APC na Jihar Bauchin, Alhaji Uba Ahmed Nana, ya ce “wannan batu a bakinku na fara ji a matsayinku na ‘yan jarida, shugabannin kananan hukumomi ne suka zabe ni?, Alummar APC na Jihar Bauchi ne suka zabe ni, kuma a tsarin mulki ba su da hurumi na dakatar da ni daga shugabancin jam’iyya.”

Dangane da batun rashin iya gudanarwa kuwa, Alhaji Uba Nana ya ce su wadannan mutane ai su ma ‘yan majalisar gudanarwa ne na jiha, don shugabannin kananan hukumomi suna cikin majalisar gudanarwar wace irin rawa suka taka?

Ya ce wadannan mutane dai sun aiwatar da kwangilarsu da aka daukesu don su aiwatar da ita amma kwangilar tasu ba za su je ko’ina ba, wannan kwangila tasu soki burutsu ne, ya ce ko kokwanto babu kan cewa sa su aka yi don shugabannin kananan hukumomi guda 20 ne ya kamata a samu, amma nawa ne suka yi wannan aiki, saboda haka su wadannan da suka yi wannan aiki ba shugabanni ba ne, anan inda nake yanzu akwai shugabannin kananan hukumomi a wajen wadancan ba shugabannin ba ne.

Jamiyyar APC a Jhar Bauchi dai tana fama da rikice-rikicen cikin gida kamar yadda ake fama da shi a takwarorinta dake wadansu jihohi, rikicin da ya fi kamari akwai rikicin dake tsakanin gwamnatin Jihar Bauchi da ‘Yan Majalisun tarayya wadda wannan rikici an kasa warware shi. Haka kuma jam’iyyar ta dakatar da Sanatan Bauchi ta Kudu Mallam Ali Wakili, da ma wadansu daga cikin fitattun ‘ya’yan jamiyyar a Jihar Bauchi.