✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Rasha da Ukraine: Amurka za ta ba wa Ukraine makamai

Amurka za ta ba wa Ukraine makaman da za ta kare kanta.

Kasar Amurka na shirin kai wa Ukraine dauki da makamai don kare kanta daga barazanar kai hari daga kasar Rasha.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, ya ce kasarsa ta yi alkawarin tallafa wa Ukraine da makaman da take kerawa na cikin gida don kare kanta daga duk wata barazana musamman daga Rasha.

Wannan dai na zuwa ne bayan kasashen Arewa maso Gabashin Turai uku sun mika wa Amurka bukatar hadin gwiwa ta neman tallafa wa Ukraine da manyan makamai.

A halin da ake ciki yanzu dai dubban dakarun Rasha na jibge a kan iyakarta da Ukraine dauke da muggan makamai suna jiran umarnin afka wa kasar.

Ko a shekarar da ta wuce, sai da Gwamnatin Joe Biden, ta tallafa wa Ukarine da kudi har Dala miliyan 450 don karfafa fannin tsaronta, sannan ta kara mata wata Dala miliyan 200 a farkon makon nan.