Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa a yanzu haka Hukumar Killata Arzikin Kasa wacce a takaice ake kira (FRC) na cikin tsaka-mai-wuya saboda yadda wasu daga cikin ma’aikatan hukumar ke zargin Mukaddashin Shugaban Hukumar, Victor Muruaka, da aikata cin hanci da rashawa
Ana zargin Muruaka aikata cin hanci da rashawa da yin sojan-gona da zamba cikin aminci da makarkashiya da kuma yawan karya dokar aiki ta shekara 2007.
An ce Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC da kuma Hukumar Yaki da Ta’annutin Kudi ta EFCC suna binciken zarge-zargen da ake yi masa bayan da wasu ma’aikatan hukumar suka yi korafi a kansa.
Lokacin da wa’adin shugabannnin gudanarwar hukumar ya kare a ranar hudu ga watan Disemban shekarar 2013, sai aka nada Muruaka, wanda mataimakin darakta ne ya jagoranci hukumar.
Aminiya ta gano cewa ana nada Muruaka a watan Janairun shekarar 2014 sai kawai ya mayar da kansa mukaddashin shugaban hukumar inda ya rika karbar albashi daidai da na cikakken shugaban hukumar.