✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rio Ferdinand zai koma damben boksin

Tsohon dan kwallon Manchester United na Ingila Rio Ferdinand ya shirya tsaf don ya koma harkar damben boksin. Ferdinand wanda shahararren dan kwallo ne a…

Tsohon dan kwallon Manchester United na Ingila Rio Ferdinand ya shirya tsaf don ya koma harkar damben boksin. Ferdinand wanda shahararren dan kwallo ne a kulob din Manchester da kuma kasar Ingila ya nuna baya ga kwallon kafa, abin da ya fi sha’awa a yanzu shi ne ya koma harkar damben boksin.

Tuni tsohon dan kwallon ya kai ziyara ga gogaggun ’yan damben boksin irin su Tyson Fury da Dabid Haye da Tony Bellew wajen neman shawararsu a game da aniyarsa ta komawa harkar damben boksin.

Ferdinand yana daga cikin ’yan kwallon da kulob din Manchester United na Ingila ba zai taba mantawa da su ba a game da irin gudunmawar da ya bayar wajen samun nasara ga kulob din.   Kafin ya koma Manchester United  ya yi kwallo a kulob din West Ham United a tsakanin shekarar 1996 zuwa 2000.  Daga nan ya koma Leeds United a tsakanin 2000 zuwa 2002 inda daga bisani ya koma Manchester United a tsakanin shekarar 2002 zuwa 2014 watau kimanin shekaru 12 sannan a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015 ne ya koma kulob din kueens Park Rangers inda daga nan ne ya yi ritaya daga buga yin kwallon kafa.

Tsohon dan kwallon da yanzu haka yake da shekara 38 ya yanke shawarar shiga harkar damben boksin ne bayan ya daina wasan kwallon kafa.

Ya halarci gasar damben boksin ta duniya da aka yi a tsakanin dan Najeriya Anthony Joshua da Klitscho a watannin baya kuma ya taya Anthony Joshua murna jim kadan bayan ya lashe gasar.