✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

“Rufin asirin da ke cikin sana’ar kira ya sa na rike ta da kyau”

Wani fitaccen makeri da ke zaune a Legas mai suna Sulaiman Bala Makeri ya ce da ya bar aikin gwamnati ne ya koma sana’ar kira.Sulaiman…

Wani fitaccen makeri da ke zaune a Legas mai suna Sulaiman Bala Makeri ya ce da ya bar aikin gwamnati ne ya koma sana’ar kira.
Sulaiman Bala Makeri, dan shekaru 45, dan asalin Jihar Kaduna ya yi furucin haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.
Ya ce, “Dayake Allah Ya kaddara zan dawo sana’ar kira, sai na bar aikin gwamnati, na yi ritaya daga inda na yi aiki, a sashen tsangayar ilimin shari’ar addinin Musulunci da ke Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a matsayin mai kula da dakin karatu. Yayin da mahaifinmu ya rasu, kuma na ga ’yan uwana babu wanda yake so ya ci gaba da sana’ar da yake yi, sai na yi ritaya na dawo na kama sana’ar gadan-gadan. Ga shi yanzu Allah Ya rufa mini asiri, ina samu alheri fiye ma da lokacin da nake aikin albashi. Ita sana’ar kira tana da wani sirri, musamman na rufin asiri, shi ya sa na rike ta da kyau. Gaskiya sana’ar ta fi aikin albashi, nesa ba kusa ba, don ni yanzu na fi samun kudi a kan lokacin da nake aikin albashi.”
Ya bayyana cewa yana sarrafa karafa iri-iri ta hanyar yin wukake da takubba da zobba da gatura da adduna da sauransu.
Ya kara da cewa  ya samu nasarori da yawa, wadanda suka hada da samun kudin daukar dawainiyar iyalinsa da na ’yan uwa da abokan arziki.
Sulaiman, wanda ya koyi sana’ar kira a wurin mahaifinsa tun yana karami, ya ce rashin ciniki shi ne babban kalubalen da yake fuskanta. “Babu shakka muna fuskantar kalubale iri-iri, kamar rashin ciniki, amma duk da haka sana’ar kira ta fi aikin albashi don kusan kullum sai ka sami kudi, amma shi aikin albashi sai wata za a ba ka”. Inji shi.