✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar Hisba ta kama mashaya da karuwai a Gujungu

Jami’an Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa sun kai samame kasuwar Gujungu, inda suka kama wadanda ake zargi mashaya ne da mata masu zaman kansu su…

Jami’an Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa sun kai samame kasuwar Gujungu, inda suka kama wadanda ake zargi mashaya ne da mata masu zaman kansu su 96 da ake zargi da aikata laifin badala.
Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa, Ustaz Aliyu Galamawa ne ya sanar wa wakilinmu haka, bayan damke wadanda zargin mashaya da karuwai ne a wasu gidajen giya a ranar Lahadin da ta gabata, a daidai lokacin da kasuwar garin take tsakiyar ci.
Ya kara da cewa, daga cikin wadanda aka kama, mutum 70 mata ne da ba a tantance matsayinsu ba, yayin da sauran 26 mata ne da aka tabbatar da cewa karuwai ne; yayin da aka samu kwalaben giya da mashayan suke kwankwada har guda 252 da kuma kwalaben giya marasa ruwan giyar guda190.
Kamar yadda ya ce, an gurfanar da mutum 48 daga cikinsu a gaban kotun Shari’ar Musulunci da ke Taura, har ma Alkali dahiru Madu ya yanke masu hukuncin bulala goma-goma da tarar Naira 5,000 kowannensu. Yayin da da sauran mutum 48 aka gabatar da su a gaban kotun Majistare da ke Taura, domin yi musu hukunci.
Tuni Majistare Sa’idu Galadima ya tura su gidan maza har sai ranar 16 ga wannan watan, domin kotun ta samu damar yin nazari a kan irin hukuncin da ya dace da su.