✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabani kan kasafin kudi ba sabon abu ba ne – Mikati

Alhaji Shuaibu Idris Mikati, tsohon babban ma’aikacin banki ne, kafin ya koma aiki da kamfanin dangote a matsayin Darakta, yanzu kuma shi ne shugaban kamfanin…

Alhaji Shuaibu Idris Mikati, tsohon babban ma’aikacin banki ne, kafin ya koma aiki da kamfanin dangote a matsayin Darakta, yanzu kuma shi ne shugaban kamfanin Tuntuba na Time-Line. Aminiya ta samu ganawa da shi kuma ga yadda tattaunawar ta kasance:

Alhaji Shuaibu Idris MikatiAminiya: A matsayinka na masanin harkar kudi, me ye ra’ayinka game da kasafin kudi da aka sanya wa hannu?
Abin murna ne yadda aka sami rashin fahimta sannan aka warware tsakanin bangaren zartarwa da  ’yan majalisa. Sannan a wanna lokaci ne dukkan wanda yake son zuba zari zai sayi jari don neman cin riba nan gaba. Sannan ’yan majalisa da dama suna da burin ganin sun ci ribar mulkin dimukradiyya kamar yadda gwamnati mai mulki ta bayyana tun lokacin zabe.
Abin la’akari ne cewa ba yadda shugaban kasa zai fitar da kudi, ba tare da yardar majalisa ba.

 Aminiya: Me ye ya jawo tsaikon da aka samu, kuma ina mafita?
 Duk da cewa ni ba dan majalisa ba ne, amma idan ka dubi abinda ke faruwa, yawancin mu ba mu yi adalci ga shugaban kasa da ’yan majalisa ba. Dalili kuwa shi ne wannan ne karon farko a tarihin kasar nan da aka sa bayanai a cikin kasafin kudi da majalisan dokoki ba ta yi takaddama a kai ba. Domin an yi hasashen  farashin gangar danyen mai a kan Dala 38, kuma za a rinka hako danyen man fetur ganga miliyan biyu da dubu 200 a kullum, za a yi musayar Naira 198 kan ko wace Dala guda da kuma cike raran gibin kasafin kudi, amma duk wadandan majalisa ba ta ce ko uffan ba a dangane da su. Ya kamata a yaba da haka.

Aminiya: A baya, an taba yin kasafin kudi da aka samu sabani?
 A mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo na farar hula, majalisa ta kwashe shekaru biyar zuwa bakwai tana takaddama da kasafin kudin da ya mika mata. Ko a lokacin mulkin marigayi Shugaba Umaru Yar’adua da na Goddluck Jonathan an samu sabani.

Aminiya: Wadanne irin kalubale aka samu da yadda za a warware su?
kalubalen da aka samu sun hada da kasafin Naira biliyan 17 na yin sabuwar hanyar titin jirgi daga Legas zuwa Kalaba. Sannan sai kalubalen zargin yin kokarin aringozon kudi daga bangaren ma’aikatan gwamnati da kuma na wanda ake ba ’yan majalisa kudi da zumman za su yi ayyukan ci gaban al’ummarsu, wato (Constituency Project). Jama’a ba za su taba yafe wa ’yan majalisar da suka rinka karbar kudin ayyuka a mazabunsu ba, wanda kuma duk salon ruf da ciki ne. Idan an gyara titunan jiragen kasa suka koma aiki gadan-gadan ’yan kasa duka za a karu matuka. Don dan majalisa yana ba da kwangila ta haka rijiyar burtsatse wacce ba ta wuce Naira dubu 700 zuwa  miliyan daya ba, a kan Naira miliyan biyu ga wani na kusa da shi don son rai kawai.

Aminiya: Me ye illar yin kasafin kudi a makare ga tattalin arzikin kasa, duk da ana zargin ba a jituwa tsakanin bangaren zartarwa da majalisa?
 ’Yan Najeriya sun yi matukan fushi da ’yan majalisa domin a lokacin da talakawa ke neman kobon da zai sayi abinci ya sa a bakin salati, wani na can ya raina karamar mota kirar Kia, sai dai don shi dan majalisa ne wai sai dai a saya masa mota ta alfarma kirar Toyota Prado ko Lankuruza, sam sam wannan bai dace ba ko kadan. Don ’yan majalisa sun mayar da masu wuni suna shan rana da sanyi don kada kuri’a ba mu san abin da muke yi ba. Kuma makon da ya wuce, ministar kudi ta ce an kashe Naira biliyan 19 kacal a kan gyaran tituna, sannan an kashe Naira biliyan 64 don tafiye-tafiye a jiragen sama irin na alfarma a waccan gwamnati. Sannan wani gwamna ya yi tafiye-tafiye har sau 230 a jirgin haya na musamman na alfarma wanda ko wace tafiya yana biyan Naira miliyan biyar na kudin al’umma ne. Amma wannan gwamnati ta sa mun ji dadi don a yanzu an hana ministoci su yi tafiya a kujera mai tsada ta alfarma. A ganina ya kamata a tsige duk gwamnan da yake barna da kudin jama’a.

Aminiya: A wannan kasafin kudin, akwai wani romo da ’yan Najeriya za su samu?
Muna fatan a kashe kudin har kwalliya ta biya kudin sabulu. Sannan a rage barnar kudi ba gyara, ba sabar. Don samun karin zuba jari. In dai an ci gaba da iya sarrafa kudi to za a gudu-tare a tsira-tare.