✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabuwa da tsohuwar PDP: ’Ya’yan PDP a Jihar Kebbi sun bukaci Gwamna dakingari ya bayyana bangaren da yake

Hatsaniyar da ke addabar Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan ya sanya magoya bayan jam’iyyar a Jihar Kebbi sun fara guna-guni dangane da rashin sanin…

Gwamna Sa’idu Dakingari na Jihar KebbiHatsaniyar da ke addabar Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan ya sanya magoya bayan jam’iyyar a Jihar Kebbi sun fara guna-guni dangane da rashin sanin alkiblar da suka nufa bayan da aka fara zargin cewa Gwamnan Jihar Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya fara yin fuska biyu, ta yadda har yanzu ba wanda ya san inda ya nufa a tsakanin sabuwar PDP da kuma tsohuwar PDP.
Wakilinmu ya ruwaito cewa tun lokacin da badakalar ta kunno kai ’yan siyasa a jihar suka kasa sanin inda Gwamna dakingari ya nufa saboda zurfin cikinsa, lamarin da ya sa wasu ke ganin har yanzu yana yin cikakkiyar biyayya ga banagaren Bamanga Tukur da ke samun goyon bayan Shugaba Goodluck Jonathan.
Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi kuma na hannun daman Gwamna dakingari da ya nemi a sakaya sunan sa ya bayyana wa Aminiya a Birnin Kebbi cewa, su yanzu Gwamna ya koya musu wayo saboda a kullum abin da ya gaya musu gobe sai ya buda musu wani shafin, saboda haka yanzu sun kusa dawowa daga rakiyarsa a fagen siyasa. “Kuma magana ta gaskiya mu yanzu sun riga mun yi matsaya, mun yanke shawarar komawa sabuwar PDP amma ba za mu fito fili mu nuna kanmu ba tukuna, amma ba gudu ba ja da baya a kan wannan ra’ayi namu,” inji shi.
Ya ce sai dai shi Gwamnan da sauran mukarabansa da ke cin moriyar tsohuwar PDP din su saura a cikinta, amma su za su tafi idan ma za su bar PDP din sai dai su bar ta, sun daina bin ra’ayin wani don amfanin kansa kadai.
Sakamakon wannan takaddama da rashin sanin inda Gwamna dakingari ya nufa ya sa lokacin da Gwamnan ya dawo daga karamin babban taron Jam’iyyar PDP a Abuja, manema labarai da suka tarbe shi a harabar Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar suka tambaye shi don jin inda ya nufa, amma sai ya ce ba zai ce da su komai ba. “Ba zan yi magana ba,”abin da Gwamna ya ce ke nan.
Sai dai yanzu ’yan siyasar jihar sun yi tsaye sai Gwamna dakingari ya yi bayanin matsayinsa a kan wannan batu, idan kuma ba haka ba su za su dauki mataki saboda siyasa ce ake yi ba mulkin soja ba inda shugaba ne kawai ke bayar da umarni kowa ya bi dole.
Wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa wadanda ke sahun gaba a sabuwar PDP sun fara neman inda za su bude ofishinsu na jiha a Birnin Kebbi, kuma ta ce za su bude ofisoshinsu a dukkan kananan hukumomi 21 na jihar.
Aminiya ta ji wata majiya na cewa rashin sanin alkiblar Gwamna dakingari ba ya rasa nasaba da rashin tasiri da gogewarsa a fagen siyasa saboda bayan dangantakarsa da ubangidansa a fagen siyasa Sanata Adamu Aliero ta fara tsami kuma a yanzu baya ga wadanda suke biyayya ga reshi don yana rike da madafun iko, kusan ba ya tare da jama’a.
Binciken Aminiya ya gano cewa tun kafin badakalar ta kunno kai, PDP a jihar ta shiga wani hali na rashin tabbas, saboda masu neman mukaman siyasa sun yi mata yawa tun daga na ’yan majalisar jiha da ta wakilai da ta dattawa zuwa na Gwamna, amma saboda zurfin cikin Gwamnan Jihar suka yyi likimo, suna jiran lokaci.
Sakamakon wannan takaddama da ta kunno kai, a tsakanin magoya bayan Jam’iyyyar PDP na Jihar Kebbi shugaban jam’iyyar na jihar Alhaji Mansur Shehu ya kira taron manema labarai a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce su a jihar duk inda Gwamna dakingari ya nufa nan suke. Wato suna tare da Shugaban Jam’iyyyar na kasa Alhaji Bamanga Tukur, kuma ya nemi magoya bayan jam’iyyar su ci gaba da ba su hadin kai.