✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabuwar doka ta ba ’yan New Zealand damar sauya jinsinsu na haihuwa

Hakan na nufin namiji zai iya komawa mace, mace ta koma namiji.

Kasar New Zealand ta zartar da sabuwar dokar da za ta ba mutanen kasar damar canza jinsin da aka rubuta musu a takardar haihuwarsu, kamar yadda gwamnati ta sanar ranar Alhamis.

A cewar Ministar Harkokin Cikin Gidan kasar, Jan Tinetti, dokar dai na nufin cewa daga yanzu ba za a bukaci ’yan kasar su gabatar da takardar likita kafin su gamsar da kotu cewa sun canza jinsinsu ba.

Ta ce, “Yau rana ce mai cike da tarihi a New Zealand. Majalisa ta zartar da dokar da za ta sa a daina nuna wariya ga masu canza jinsi.

“Sauyin zai kuma taimaka wa matasa su yanke shawara kan jinsin da suke so a rika alakanta su da shi.

“Hakan zai ba su damar yanke wa kansu shawara, ya bunkasa lafiyar kwakwalwarsu, sannan ya inganta lafiyarsu,” inji ta.

Sai dai ta ce ’yan kasar da aka haifa a ketare ba za su ci gajiyar dokar ba, saboda masu takardar shaidar haihuwa ta kasar kadai ta shafa.

Amma ta ce za a yi aiki don magance wannan matsalar a nan gaba, bayan an fara tattauanwa da wadanda abin ya shafa.

“Dokar za ta fara aiki nan da wata 18, don a ba gwamnati damar tattaunawa da dukkan al’ummomi don tabbatar da cewa ta yi daidai da bukatun al’umma,” inji Minista Jan. (NAN)