✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sada zumunta a Musulunci

Ma’anar sada zumunta: Sada zumunta shi ne kyautatawa da jinkai da bibiyar ’yan uwa (dangi), ta hanyar sadar da dukkan alheri gare su da kawar…

Ma’anar sada zumunta:

Sada zumunta shi ne kyautatawa da jinkai da bibiyar ’yan uwa (dangi), ta hanyar sadar da dukkan alheri gare su da kawar da dukkan sharri daga gare su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk bangare ne na sada zumunta.

Har ila yau, ma’anar zumunta na game yin sallama ga dan uwa yayin haduwa da gaishe shi da ce masa ‘Yarhamukallahu’ idan ya yi atishawa ya ce ‘Alhamdulillahi.’

Sannan zuwa duba dan uwa yayin da yake rashin lafiya da jajanta masa kan wata asara da ya yi da taya shi farin cikin samun wani alheri da rufa masa asiri da rike amanarsa da kare mutunci da martabarsa a kan idonsa ko a bayansa a boye ko a bayyane da yi masa nasiha da shawara ta alheri duk sada zumunta ne.

Hukuncin sada zumunta:

Wajibi ne Musulmi su sada zumuntar da ke tsakaninsu, kamar yadda shiryarwar Musulunci ta ginu a kai, Allah Ta’ala Yana cewa: “Ka tuna lokacin da Muka riki alkawari daga Bani Isra’ila cewa kada su bauta wa kowa sai Allah, kuma su kyautata ga iyaye da ma’abutan zumunta (’yan uwa ko dangi) da marayu da miskinai, kuma ku gaya wa mutane kyakkyawan zance, kuma ku tsayar da Sallah ku ba da Zakka, sai kuka juya baya (ga barin wannan umarni), sai ’yan kadan ne daga cikinku, kuna masu bijirewa.”

Kuma a Suratul Bakara, aya ta 27 Allah Ya fassara fasikai a cikin fadinSa: “Su ne masu warware alkawarin Ubangiji (kan aiko Annabi (Sallallahu Alaihi Wassalam), bayan karfafa alkawarin gare su, kuma suke yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (zumunta), kuma suke barna a bayan kasa,wadannan su ne tababbu.”

Haka nan kuma a Suratur Ra’adi aya ta 21, Allah Ya bayyana ma’abuta hankali da cewa: “Kuma su ne masu sadar da abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (na zumunta), kuma suke jin tsoron Ubangijinsu, kuma suke jin tsoron mummunan hisabi.”

Hadisai sun bayyana muhimmancin zumunta, kamar yadda Buhari da Muslim suka ruwaito daga Sayyidina Jubairu dan Mud’im (R.A), ya ce: “Annabi (Sallallahu Alaihi Wassalam), ya ce: “Mai yanke zumunta ba zai shiga Aljanna ba.”

Ma’abuta zumunta: Su ne duk makusantan mutum (na jini) na kusa ko na nesa, magadansa ne ko ba magada ba, muharramai ne ko ba muharramai ba, masu dangantaka da shi da suka hada da kakanni da iyaye da ’ya’ya da jikoki, ’yan uwa maza ko mata kanne da yayye da ’ya’yansu da ’yan uwan uba da na uwa.

Idan muka fadada ma’anar zumunta zuwa ga ’yan uwantakar Musulunci da ba da hakki ga ma’abutansa, to kai-tsaye, aya ta 36 a Suratun-Nisa’i, za ta yi mana jagora ga raba ma’abuta hakkin kyautatawa zuwa gida uku, inda Allah Madaukaki Yake cewa:

“Kuma ku bauta wa Allah, kada ku hada wani da Shi a cikin bauta (shirka), kuma ku kyautata ga iyaye da ma’abucin zumunci da marayu da miskinai da makwabci ma’abucin zumunci da makwabci manisanci da aboki a gefe da dan tafarki da bayinku. Hakika Ubangiji ba Ya son wanda ya kasance mai takama, mai yawan alfahari.”

Bisa koyarwar wannan aya, za mu iya raba ma’abuta hakkin a kyautata musu zuwa gida uku:

a). Mutum mai hakki uku: Dan uwa na jini, Musulmi kuma makwabci.

b). Mautum mai hakki biyu: Musulmi kuma makwabci.

c). Mutum mai hakki daya: Makwabci a gida ko a kasuwa ko abokin tafiya da ba Musulmi ba.

Falalar sada zumunta:

Falalar sada zumunta ba za ta kayyadu ba, sai dai kawai a fadi kadan daga ciki:

  1. Tsawaitar rayuwa.
  2. Wadatar zuciya.
  3. Bunkasar dangi.
  4. Tsallake Siradi cikin sauki.
  5. Samun yardar Allah.
  6. Samun hadin kai.
  7. Samun shiga Aljanna da sauransu.

Kuma yawanci wadannan falalolin an ciro su ne daga Hadisan Annabi (Sallallahu Alaihi Wassalam), kamar haka:

Hadisin Muslim daga Abu Huraira (RA) cewa, Annabi (Sallallahu Alaihi  Wassalam), ya ce: “Wanda ya kasance ya ba da gaskiya ga Allah da Ranar Lahira, to ya sadar da zumuncinsa.” A wata ruwaya tasa kuma ya ce: “Wani mutum ya ce da Annabi (Sallallahu Alaihi Wassalam), ya Ma’aikin Allah! Ina da makusanta, ina sadar musu zumunta, amma suna yanke min ita, ina kyautata musu suna munana min, ina yin afuwa gare su suna yi min wauta. Sai Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wassalam), ya ce: “In dai ka kasance kamar yadda ka fada, kamar kana rabauta daga gare su ne bisa bakin zunubin da suke aikatawa, to, taimako daga Allah ba zai gushe ba a tare da kai game da su, matukar ka dawwama a kan haka.”

A wata ruwayar Buhari daga Sayyidina Abu Huraira (RA), ya ce Ma’aiki (Sallallahu alaihi Wassalam), ya ce: “Ba mai sada zumunta ba ne, wanda in an je masa ya je, sai dai mai sada zumunta shi ne wanda in an yanke masa zumuntar, sai ya sadar da ita.”

Sayyidina Anas (RA) ya rawaito Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa: “Wanda yake so a yalwata masa arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to ya sada zumuntarsa.” (Buhari da Muslim suka ruwaito). Har ila yau sun kara ruwaitowa daga Nana A’isha (RA) daga Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wassalam), ya ce: “Zumunta tana makale a jikin Al’arshi, tana cewa: “Wanda ya sadar da ni, Allah Ya sadar da shi, wanda kuma ya yanke ni, Allah Ya yanke shi!”

Nana Asma’u ’yar Sayyidina Abubakar (RA) ta ce: “Mahaifiyata ta zo min, kuma mushrika ce a zamanin Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wassalam), sai na tambaye shi cewa: “Mahaifiyata ta zo min kuma tana kwadayin wani abu a wurina, shin na iya sada zumuntarta?” Sai ya ce: “Kwarai, ki sada zumuntar mahaifiyarki.” (Buhari da Muslim suka ruwaito).  Har yau sun fitar daga Abu Ayyuba Khalid dan Zaidil Al’ansari (RA) cewa wani mutum ya ce: “Ya Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wassalam)! Ba ni labarin aikin da zai shigar da ni Aljanna, ya nesanta ni daga wuta. Sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wassalam), ya ce: “Ka bauta wa Allah, kada ka yi shirka da Shi, ka tsayar da Sallah ka ba da Zakka, sannan ka sada zumunta.”

Ukubar yanke zumunta:

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, shi ne abin da za mu iya cewa, saboda abin da ya samu zumunta na balbalcewa a yau. Babu zumunta, dan uwa ya ga dan uwansa, kowa ya shige, saboda rashin sani, ko a kan sani. Ba a zumunci, mai kudi don girman kai da ganin ya isa, sai dai shi a zo masa, talaka kuma don tsoron wulakanci ba zai je ba, talaka da talaka kuma don tsoron kada ya dora wa dan uwansa nauyi ya ki sada zumunta.

Ayoyi da Hadisai da dama, sun ja kunne kan yanke zumunta. Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wassalam), ya ce: “Mai yanke zumunta ba zai shiga Aljanna ba.” Buhari da Muslim daga Jubairu dan Mud’im.

Hanyoyin sada zumunci:

Ana sada zumunta ce ta hanyoyi da dama, kamar tattaki zuwa wurin ’yan uwa ko wasika ko wayar sadarwa ko sakon baka (a aika gare su) ko shirya tarurrukan taya farin ciki ko jajanta wa wani.

Allah Ya inganta zumuntar da ke tsakanin Musulmi.

Habibu Muhammad Ayagi

Raudhatur-Rasul, Ayagi, Kano

07082460196

Imel: [email protected]