✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sadaka

Wani mutum ne yana zaune a masallaci, sai wani mabukaci yana neman taimako, sai ya dauko Naira 10 ya mika masa. Ya ba shi ke…

Wani mutum ne yana zaune a masallaci, sai wani mabukaci yana neman taimako, sai ya dauko Naira 10 ya mika masa. Ya ba shi ke nan sai ya ji wani mutum ya taba shi a baya. Yana waigawa sai ya ga wani mutum a bayansa, ya mika masa Naira dubu biyu. Shi kuma yana amsa sai ya kira mabukacin nan ya sake mika masa su duka. Bayan an fito daga masallaci, sai mutumin nan ya ce wa wanda ya bayar da sadakar cewa: “Wannan Naira dubu biyu da na miko maka, naka ne suka fado daga a aljihunka, a lokacin da kake ciro Naira 10 za ka bayar sadaka.”

Daga Yasriba Fagge Kano, 08112261006