✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saka da mugun zare a Jihar Taraba: Dimokradiyya ko haukadiyya?

Wani abu sai Najeriya! Idan ba Najeriya ba, wace kasa ce za a dauki tsawon lokaci, malaman jami’a na zaune durshan a gida, dubban dalibansu…

Jirgin da Gwamna Suntai ya yi hadari da shi a baraWani abu sai Najeriya! Idan ba Najeriya ba, wace kasa ce za a dauki tsawon lokaci, malaman jami’a na zaune durshan a gida, dubban dalibansu na zaman kashe wanduna, amma gwamnatin kasar ko gezau? Idan ba kasata Najeriya ba, ina ne za ka ga ana mulkin haukadiyya da sunan dimokradiyya? Ina ne masu mulki da mukarrabansu da iyalansu ke tufka tsiyar da suka ga dama? Wannan haukadiyya sai a kasata, inda da zarar matar Shugaban kasa ta bushi iska, sai ta tsiri wani taro na ba-gaira-ba-dalili, ta rufe titin al’umma ruf, har sai ta gama sannan mutane su samu zarafin kansu.
Ba wannan ba ma, idan ba kasata Najeriya ba, ina ka taba jin maridi ya kasance a gadon mulki? Kuma har ma yana korar mukarrabansa da suka rike masa amana, suka rike al’ummarsu? Idan ba a kasata ba, ina ne za ka ga matar gwamna da ’yan kanzaginta suna yawo da hankalin al’ummar jiharsu? Wannan kwamacala sai a kasata Najeriya.
Bari in daina bugun taiki, in bugi jakina kai tsaye. A wannan tsokaci, na kuduri aniyar bin kadin hagunguntun al’amuran da a yanzu haka suke faruwa a Jihar Taraba, al’amuran da suka daure mani kai. Ba ni kadai ba ma, har da duk wani mahalukin da ya mallaki hankalinsa.
Kafin sannan, bari mu dan koma baya, mu yi tariyar abubuwan da suka faru watanni goma da suka gabata. A watan Oktoban bara ne Gwamnan Jihar Taraba, danbaba danfulani Suntai ya yi hadari da jirgin sama mallakinsa, a yayin da yake tukawa da kansa. A sanadiyyar haka ne ya jikkata, kwakwalwarsa ta tabu, aka dauke shi ranga-ranga zuwa wani asibitin kasar Jamus, inda bayan ya yi watanni yana amsar magani, aka canja masa asibiti zuwa Amurka.
A lokacin da mai girma gwamna ke markabun jinya a kasashen waje, yana neman Allah Ya sawwake masa jarabawar da ya samu kansa ciknta, a bangare daya kuma nan gida Jalingo, wasu daga cikin iyalansa sun takarkare suna neman hanyar da za su cusa masa bakin ciki. Bakin ciki mana, domin kuwa mutumin da ke jinya, amma za a ci gaba da amfani da sunansa ana dibar masa ukuba?!
Bari in warware wannan zaren da na kulla. A lokacin da Suntai ke jinya, wasu daga iyalansa tare da hadin bakin wasu karkatattun ’yan siyasa, sai suka dauki al’amarin, suka mayar da shi wata kafa da za su bi su cin ma bakaken muradunsu. Na daya, sun mayar da laulayin gwamnan wata kafa ta haddasa rashin jituwa tsakanin al’ummar Jihar Taraba. Sun samu nasarar haka ne ta amfani da addini, inda suka rika nuna cewa al’ummar Musulmin Taraba kamar suna murna da abin da ya samu gwamnan, kasancewarsa mabiyin addinin Kirista ne. Duk kuwa da cewa al’ummar jihar sun yi watsin karan mahaukaciya da wannan kitimirmira, kasancewar ’yan uwan juna ne. Ko ba komai, akwai auratayya da zumunci mai karfi da ke tsakanin mabiya addinan biyu a jihar, don haka masu neman amfani da wannan dama domin su haddasa gaba a tsakanin al’ummar jihar ba su samu nasara ta wannan fuska ba.
Tsiyar nasara sai za shi gida. Mukarraban nan da suka lura da cewa talgensu zai yi ruwa, sai suka sake bullo da wata tsiyar. A wannan karon, bayan gwamnan ya share watanni goma a waje, yana amsar magani, sai suka jajibo shi, suka dawo da shi gida cikin wani wulakantaccen yanayi. A shirinsu, duk da ba ya iya tsinana wa kansa komai, duk da cewa an samu tabbacin cewa ko maganar kirki bai iya yi, amma suna son a ce ya dawo kujerar mulki, koda kuwa mulkin baba-na-daka-gemu-na-waje za a gudanar. Sai dai, idan haka ta tabbata, anya an yi wa al’ummar Jihar Taraba adalci? Anya wani abin kirki zai iya biyo bayan wannan bahallatsa?
 Ba wannan ba ma, ko abin da ya faru a Lahadin da ta gabata ya dace da hankali? Ya dace da mutunci da kamalar dan Adam? Kamar yadda al’marin ya faru, lokacin da jirgin gwamnan ya sauka a Jalingo, mukarrabansa ne suka yi uwa da makarbiya wajen tarbarsa da kuma daukar matakan hana al’ummar da suka zabe shit un farko. A rirrike suka sauko da shi daga jirgi, yana tangal-tangal kamar zai fadi. An hana ’yan jarida matsawa kusa da shi, balle ma su nemi jin ta bakinsa, idan har yana ya maganar. An hana Mukaddashin Gwamna sukutun ganawa da shi. Sai aka kunshe shi a mota zuwa gidansa, daga nan babu wanda ya kara jin duriyarsa.
Shugaban Majalisar Jihar Taraba, Haruna Tsokwa, shi ma ya nuna takaicinsa game da wannan mataki da mukarraban gwamnan suka dauka. Ya bayyana wa manema labarai cewa shi kansa da sauran ’yan majalisar jihar sun yi kokarin ganinsa, amma mukarrabansa sun hana. Idan ba Najeriya ba, ina za a ce an yi haka? Mulkin dimokradiyya ne wannan ko kuwa na haukadiyya?
A tarihin rashin lafiyar gwamnoni a Najeriya, danbaba Suntai ba shi ne na farko ba, amma ba a taba samun wanda aka yi amfani da laulayinsa wajen cin ma bakin kuduri ba kamarsa. A can baya, Gwamnan Jihar Inugu, Mista Sulliban Chime, ya taba tafiya kasar waje neman magani, ya dade bai dawo ba, amma da ya dawo, an yi masa kyakkyawar tarba kuma ya yi wa al’ummarsa jawabi, sannan ya ci gaba da gudanar da harkokinsa gaban jama’a. Me ya hana Gwamnan Jihar Taraba yin kamar haka? Dalili shi ne, ga dukkan alamu bai warke ba kuma ba zai iya gudanar da mulkin jama’a ba a yanayain da yake.
Mukarraban Gwamna Suntai sun samu nasarar dasa wata irin bahaguwar dasisa a zukatan al’umma. Haka kuma sun samu nasarar tayar da guguwar jita-jita da zullumi, kamar kuma yadda suka kara bude kafar wulakanta shi kansa gwamnan da keta mutuncinsa. Haka ta faru ta hanyoyi da dama, musamman ma yadda aka yi ta yada jita-jita a dandalin Facebook, ana cewa wai gwamnan yakan yi dariya sau 600 a rana, alhali lafiyayyen jariri ma sau 200 kadai yake dariya. Wannan yana nuna cewa gwamnan bai da lafiyar kwakwalwa. Wanda ke cikin irin wannan yanayi, anya zai iya gudanar da mulkin jiha kamar Taraba a dimokradiyyance? A’a, sai dai idan salon mulkin haukadiyya ake son gudanarwa!
Wani batun kuma da aka yi ta yadawa a wannan dandali na Facebook shi ne, a ranar da aka dawo da shi, sai da ya gartsa wa matarsa cizo a hannu. Ba wani abu ya karfafa irin wadannan labarai ba, sai irin yadda mukarraban gwamnan suka ba da kafar haka. Kuma lallai abin bai dace ba.
Al’ummar Taraba dai mutane ne masu hankali da tunani, mutane ne masu ilimi kuma masu wayewa. Ba na tunanin za su bari wasu kalilan daga mukarraban Suntai su yi masu wawa-ci-ka-tashi. Hakan ta tabbata inda kungiyar ‘Taraba Justice Forum’ (kungiyar Tabbatar Da Adalci A Taraba) ta y fara yunkurin yaki da mukarraban Suntai.
kungiyar ta sayi shafi na 32 na jaridar Daily Trust ta ranar Laraba, 28 ga Agusta, 2013, inda suka jaddada kukansu ga al’umma kamar haka:
 Sun yi kira ga Shugaban kasa da ya shiga tsakani, ya gyara al’amuran Jihar Taraba. Sun yi kira ga Majalisar Tarayya, ita ma ta yi nata yunkuri wajen daidaita lamarin. Sun yi kira ga Majalisar Jihar Taraba da ta fara yunkurin tsige Gwamna Suntai, idan har bai bayyana gabanta ya yi masu jawabin halin da yake ciki ba. Sun kuma yi kira ga al’umma gaba daya, da su yi wani abu, kafin Jihar Taraba ta fada cikin tsomomuwa.
Ga alama kiran nasu ya fara samun tagomashi, inda kwararren lauyan nan mai fafutukar kare hakkin al’umma, Femi Falana ya fito fili ya kalubalanci takardar da aka ce wai Gwamna Suntai ya aika wa Majalisar Jihar Taraba, inda yake nuna cewa wai ya dawo. Lauyan ya nemi Sufeto-Janar da ya gudanar da kwakkwaran bincike, domin gano wadanda suka yi sojan-gona, suka rattaba hannu a wasikar da miyan Gwamna Suntai, domin kuwa ana zargin cewa abin da mukarraban gwamnan suka yi ke nan.
Ya kamata dai a taka wa mukarraban Gwamna Suntai burki tun kafin su susuntar da kimar al’ummar Jihar Taraba. Idan ba a taka masu burki ba, to kuwa mulkin jihar zai tashi daga na dimokradiyya, zai koma na haukadiyya. Allah Ya kiyaye.
***
A labarin farin ciki kuwa, Bagizage Sunusi Skipper Kura, Jihar Kano 08035946169, ya samu karuwa, inda amaryarsa ta Haifa masa jariri a Talatar da ta gabata. (Allah Ya raya shi, Ya sanya mai albarka ne ga iyayensa da al’umma baki daya. Amin). – Gizago.