✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakandaren Kaduna ta zama zakara a gasar kwallon kwando na kamfanin Milo

Makarantar sakandaren gwamnati da ke Unguwar Barnawa a Jihar Kaduna da ta sakadaren ’yan mata da ke Unguwar Amarata a Jihar Bayelsa sun lashe gasar…

Makarantar sakandaren gwamnati da ke Unguwar Barnawa a Jihar Kaduna da ta sakadaren ’yan mata da ke Unguwar Amarata a Jihar Bayelsa sun lashe gasar kwallon kwando da kamfanin Milo ya shirya na rukunin maza da mata na shekarar 2015.

Gasar wacce aka gudanar a karshen makon da ya gabata a sashen wasan kwallon kwando na filin wasa na kasa da ke Legas ya bai wa ’yan kallo sha’awa.
Rukunin maza na makarantar sakandare ta Barnawa sun lallasa abokan hamayyarsu na sakandaren Siant Peters da ke garin Idah a Jihar Kogi da ci 51 da 52.
Inda sakandaren ’yan mata ta Jihar Bayelsa da ta yi nasara a kan abokiyar karawarta ta kwalejin Idia da ke garin Binin a jihar Edo da ci 18 da 15 inda suka samu kyautar gwalagwalai.
Da farko sai da sakandare ta unguwar Illupeju da ke Legas wacce sakandaren Jihar Kogi ta lallasa a wasa na kusa da karshe suka lallasa sakandaren Augustine Seminary da ke garin Ezzamgbo a Jihar Ebonyi da ci 55 da 33 inda suka zo na uku a bangaren maza.
A daya bngaren sakandaren gwamnati da ke garin Numan a Jihar Adamawa ce ta doke makarantar gwamnati ta mata da ke garin Bida a Jihar Neja da ci 31 da 29 inda suka samu kyautar tagulla a bangaren mata.
Makarantar Janaral Murtala da ke garin Yola a Jihar Adamawa ta lallasa Kwalejin Saint Joseph da ke garin Nyimah a Jihar Binuwe da ci 20 da 0 inda suka zo na biyar a bangaren maza.
Sannan kuma makarantar ’yan mata ta gwamnati daga garin Ibadan a Jihar Oyo ta doke makarantar gwamnati ta ’yanmata da ke Jogana a Jihar Kano da ci 37 da kuma 12 inda suka zo na biyar.
Banda jimillar Naira dubu 200 da kowace makaranta da ta kai matakin karshe ta samu, makarantar sakandare da ke Barnawa a Jihar Kaduna ta tafi gida da Naira dubu 150 inda sakandaren jihar Kogi ta samu Naira dubu 120 ita kuwa Legas mai masaukin baki ta samu Naira dubu 100.
dalibi Lanky Dabid Isa na sakandaren Barnawa da ke Kaduna ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi kuzari da kokari.
Mafi yawan daliban da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana farin cikinsu da samun damar nuna bajintarsu a gasar.
daliban da suka yi kokari sun bayyana farin cikinsu da samun nasara a gasar wadanda kuma ba su samu nasara ba sun bayyana cewa suna da kwarin gwiwar yin nasara a duk lokacin da suka samu damar shiga gasar.